Yayinda ake rikici a Kano, an rantsar da sabbin Shugabannin Jam'iyar APC na jihar Gombe

Yayinda ake rikici a Kano, an rantsar da sabbin Shugabannin Jam'iyar APC na jihar Gombe

  • An rantsar da sabbin shugabannin APC a jihar Gombe
  • Jam'iyyar APC na gudanar da aben shugabanninta na jiha gabanin taron gangami na kasa gaba daya
  • A jihar Kano kuwa, har yanzu ba'a gudanar da zaben ba tukun, siyasar ta canza zani

Gombe - Yayinda siyasar jihar Kano ta dau sabon salo gabanin zaben shugabannin jam'iyyar APC, an rantsar da sabbin shugabannin jam'iyyar na jihar Gombe.

Gwamnan jihar, Muhammad Inuwa, ya halarci bikin rantsar da sabbin shugabannin jam'iyyar.

Inuwa ya yi kira ga yan Jamiyar da su Zan tsintsiya madaurinki daya kamar yadda taken Jam'iyar APC ya nuna.

A jawabin da hadimin gwamnan na sabbin kafafen yada labarai, Abdul NoShaking, ya saki, ya bayyana cewa gwamnan ya umurci sabbin shugabannin su tabbatar da jam'iyyar tayi nasara.

Read also

Kano da sauran jihohi 7 da aka samu rabuwar kai a APC, aka zabi shugabanni 2 a jiha

Yace:

"A Yau Ne Gwamnan Jihar Gombe Ya Sheda Rantsar Da Sabbin Shugabanin Jam'iyar APC Na Kananan Hukumomi

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan Jihar Gombe Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya (Dan Majen Gombe) Ya umurci Sabbin Shugabanin Jam'iyar APC Na Kananan Hukumomi Dasu Yi Tsayuwar Daka Wajen Ganin Nasarar Jamiyar A Dukkan Matakai.
Gwamnan Jihar Yayi Wannan Umurni Ne Yayin Rantsar Da Sabbin Shugabanin Jam'iyar APC Na Kananan Hukumomi A Sakatariyar Jamiyar A Garin Gombe."

Yayinda ake rikici a Kano, an rantsar da sabbin Shugabannin Jam'iyar APC na jihar Gombe
Yayinda ake rikici a Kano, an rantsar da sabbin Shugabannin Jam'iyar APC na jihar Gombe Hoto: Abdul No Shaking
Source: Facebook

Ya kara da cewa wadanda suka yi jawabin a wajen rantsarwan sun hada da tsohon Dan Majalisar Wakilai Honourable Khamisu Mai Lantarki, Shugaban Jam'iyar APC Na Jihar Gombe Mr. Nitte Amangal, Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jiha Hon. Siddi Buba, Da Shugaban Dattawa Na Jamiyar Alhaji Jauro Tela JT Abubakar.

Sanatoci 3, yan majalisar wakilai 4, sun hada kai don kwace mulkin APC hannun Ganduje

Read also

An yi ittifaki kan Shema, Suleiman Nazif, da Ayu matsayin mutum 3 da zasuyi takarar kujeran shugaban PDP

Sanatocin dake wakilatar jihar Kano gaba daya da wasu yan majalisar dokokin tarayya sun hadu a gidan tsohon gwamnan jihar Kano dake birnin tarayya Abuja.

An bayyana cewa yan majalisun sun hadu ne domin kwace mulkin jam'iyyar APC hannun gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje yayinda ake shirin zaben shugabannin jam'iyyar, majiyar PoliticsDigest.

Hadimin Buhari na sabbin kafafen yada labarai, Bashir Ahmad, ya bayyana haduwan yan siyasan inda yace siyasar Kano ta dau sabon salo.

Source: Legit

Online view pixel