Sanatoci 3, yan majalisar wakilai 4, sun hada kai don kwace mulkin APC hannun Ganduje

Sanatoci 3, yan majalisar wakilai 4, sun hada kai don kwace mulkin APC hannun Ganduje

  • Siyasar jihar Kano ta dau sabon salo a yau ranar Laraba
  • Wasu manyan jiga-jigan siyasar jihar sun hadu a gidan Malan Shekarau
  • Ana zargin cewa suna kokarin kwace ragamar mulkin APC ne a jihar

Abuja - Sanatocin dake wakilatar jihar Kano gaba daya da wasu yan majalisar dokokin tarayya sun hadu a gidan tsohon gwamnan jihar Kano dake birnin tarayya Abuja.

An bayyana cewa yan majalisun sun hadu ne domin kwace mulkin jam'iyyar APC hannun gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje yayinda ake shirin zaben shugabannin jam'iyyar, majiyar PoliticsDigest.

Hadimin Buhari na sabbin kafafen yada labarai, Bashir Ahmad, ya bayyana haduwan yan siyasan inda yace siyasar Kano ta dau sabon salo.

A cewarsa:

"Wasu daga cikin jagororin jam’iyyarmu ta APC a Kano, sun ziyarci ofishin jam’iyyar na kasa a safiyar yau a Abuja. Siyasar Kano a baya-bayan nan na daukar sabon salo..."

Kara karanta wannan

Gwamnoni, jiga-jigan APC, PDP 7 da EFCC ke bincika kan batun Pandora Papers

Sanatocin dake hallare sun hada da Kabiru Gaya (APC-Kano ta Kudu), Ibrahim Shekarau (APC-Kano ta tsakiya) da Barau Jibrin (APC-Kano ta Arewa)

Mambobin majalisar sun hada da Shugaban kwamitin tsaro na majalisar Sha’aban Sharada (APC-Kano Municipal), Tijjani Jobe (APC-Dawakin Tofa/Tofa/Rimingado); Haruna Dederi (APC-Karaye/Rogo) and; Nasiru Auduwa (APC-Gabasawa/Gezawa).

Sanatoci 3, yan majalisar wakilai 4, sun hada kai don kwace mulkin APC hannun Ganduje
Sanatoci 3, yan majalisar wakilai 4, sun hada kai don kwace mulkin APC hannun Ganduje Hoto: Politicdigest
Asali: UGC

Me yasa suka hadu?

Majiyoyi daga cikin ganawar sun bayyana cewa daga cikin abubuwan da aka tattauna a ganawar shine yadda gwamnan jihar Abdullahi Ganduje, yayi babakere kan dukiyoyin jihar da lamuran jam'iyyar don kansa da iyalansa.

Saboda haka ana shirin ceto ta daga hannunsa.

Wani na ciki wanda ya bukaci a sakaye sunansa yace Sanatoci da yan majalisar sun ambaci almundahana da dukiyoyin jihar.

Har yanzu kan APC hade yake

Karin bayani kan haka, Bashir Ahmad, ya bayyana cewa akwai kalubale a siyasar jihar amma dai kansu hade yake.

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda jami’an yan sanda suka tsere yayin da yan bindiga suka mamaye fadar sarkin Ogun yayin taron APC

Yace:

"Kwarai akwai kalubale, amma har yanzu kan ‘yayan jam’iyyar APC a Kano a hade yake. Wato TSINTSIYA madaurin mu daya, karkashin jagorancin jagoran tafiyar mu."

Asali: Legit.ng

Online view pixel