An yi ittifaki kan Shema, Suleiman Nazif, da Ayu matsayin mutum 3 da zasuyi takarar kujeran shugaban PDP

An yi ittifaki kan Shema, Suleiman Nazif, da Ayu matsayin mutum 3 da zasuyi takarar kujeran shugaban PDP

  • Shugabannin PDP na Arewa sun yanke shawarar hada kai gabanin zaben 30 ga Oktoba
  • An bukaci yankunan Arewa 3 su gabatar da mutum daya-daya
  • An gudanar da kwarya-kwaryar zabe cikin yan takara 10

Abuja - Adadin masu takarar neman kujeran Shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP ya sauko daga goma zuwa uku bayan an bukaci kowani yanki cikin yankunan Arewa uku su gabatar da mutum daya.

Tsohon Shugaban majalisar dattawa, Iyiochia Ayu, a ranar Talata ya zama dan takarar da zai wakilci yankin Arewa maso tsakiya bayan Sanata David Mark ya hakura.

Hakazalika tsohon gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Shema, ya zama wanda zai wakilci Arewa maso yamma bayan lashe kwarya-kwaryar zaben da akayi tsakaninsa da tsohon gwamnan Kaduna, Ahmed Makarfi.

Yayinda Shema ya samu kuri'u 6, Makarfi ya samu kuri'a guda kacal, Kaduna, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Da alamu dan tsagin Aisha Buhari zai ci zaben shugabancin APC a Adamawa

A yankin Arewa maso gabas kuwa, Sanata Suleiman Nazif, wanda dan jihar Bauchi ne ya zama wakilin yankin a zaben.

Yan takaran zasu hadu da juna daga baya domin ittifaki kan mutum daya idan zai yiwu gabanin zaben ranar 30 ga Oktoba, 2021.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An yi ittifaki kan Shema, Suleiman Nazif, da Ayu matsayin mutum 3 da zasuyi takarar kujeran PDP
An yi ittifaki kan Shema, Suleiman Nazif, da Ayu matsayin mutum 3 da zasuyi takarar kujeran shugaban PDP Hoto: PDP
Asali: Twitter

‘Yan siyasan Arewa 10 da ke kan gaba wajen neman kujerar shugaban Jam’iyyar PDP

A baya mun kawo muku cewa yan siyasa goma ne suka bayyana niyyar takara a zaben shugabancin jam'iyyar ta PDP.

Daga cikinsu akwai tsaffin gwamnoni, tsaffin Sanatoci da kuma tsaffin masu mukami a PDP.

Ga jerinsu:

1. Sanata Ahmad Makarfi

2. Sanata David Mark

3. Muazu Babangida

4. Ibrahim DanKwambo

5. Ibrahim Shema

6. Dr. Iyorchia Ayu

7. Farfesa Jerry Gana

8. Suleiman Nazif

9. Dino Melaye

10. Alhaji Sule Lamido

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng