Babban limamin garin Agaie ya rasu yana da shekaru 91

Babban limamin garin Agaie ya rasu yana da shekaru 91

A ranar Talata, 17 ga watan Satumba ne aka yi jana’izar babban limamin garin Agaie na jahar Neja, Sheikh Ahmadu Ndanusa bayan rasuwarsa a ranar Litinin, 16 ga watan Satumba, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Sheikh Sani Abdulkadir Zaria ne ya jagoranci sallar jana’izar a gaban manyan mutane da suka samu halartar jana’izar kamarsu Etsu Agaie, Alhaji Yusuf Nuhu, Etsu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar, Sarkin Lapai, Alhaji Umar Bago da kuma manyan limaman Bida, Lapai da Doko.

KU KARANTA: Yadda wata budurwa ta burma ma Saurayinta wuka, ta kashe shi har lahira

An haifi marigayin ne a zamanin Sarkin Agaie na shida, Etsu Abdullahi, wanda ya yi mulki daga shekarar 1926 zuwa 1935, haka nan ya yi karatu a gaban malamai daga ciki da wajen jahar Neja, har zuwa Zaria.

Daga cikin malamansa akwai Malam Shehu Babango da Sheikh Abdulkadir Zaria, haka zalika ya rasu yana da yana da mata 1 da yara 17 da jikoki 106, daga cikin yaransa akwai wani babban malami dake garin Zaria, Sheikh Danlami Muhammadu Sani.

A wani labarin kuma, gwamnatin jahar Neja ta sanar da biyan hukumar shirya jarabawar kammala karatun sakandari ta NECO bashin kudi N200m domin ta sako sakamakon jarabawar daliban jahar da suka kai mutum 30,000.

Kaakakin gwamnan jahar Neja, Mary Berje ce ta bayyana a ranar Talata a garin Minna, inda tace a cikin shekaru uku da suka gabata, gwamnatin ta kashe kudin daya kai kimanin naira biliyan 1 wajen samar da ilimi kyauta ga daliban jahar Neja.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: