Adon da Aisha Buhari Ta Caba a Bikin Al'adun Kalaba Ya Ja Hankali

Adon da Aisha Buhari Ta Caba a Bikin Al'adun Kalaba Ya Ja Hankali

  • Tsohuwar Uwargidar Shugaban Ƙasa, Aisha Buhari ta halarci bikin al'adun Kalaba na 2024 cikin kyan gani da kamala
  • Bikin ya samu halartar gwamnonin Kwara da Kogi, 'yan majalisar dokoki, da jakadun kasashen waje
  • Gwamnan jihar Cross River ya jaddada cewa taken taron na bana na da nufin haɗa kai da ci gaban tattalin arziki

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasa, Aisha Buhari ta bayyana cikin kyakkyawar shiga a bikin al'adun Kalaba na 2024 da aka gudanar a ranar Asabar.

Aisha Buhari ta halarci bikin cikin tsari da kamala, ta zauna a cikin sahun manyan baki domin kallon kyawawan raye-raye da faretin ƙungiyoyin da suka mamaye titunan Calabar.

Aisha Buhari
Aisha Buhari ta halarci bikin al'adu a Kalaba. Hoto: El-Masjid Abdul Umar
Asali: Facebook

A cewar rahoton Premium Times, gwamnonin Kwara da Kogi, AbdulRahman AbdulRasaq da Ahmed Ododo, da wasu ‘yan majalisa da jakadun kasashen waje suma sun halarci bikin.

Kara karanta wannan

Tsohon hadimin Jonathan ya soki El Rufa'i kan zargin kabilanci a gwamnatin Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aisha Buhari ta ƙayatar a bikin al'adu

Aisha Buhari ta bayyana cikin kyakkyawan sutura mai ruwan hoda wacce ta jawo hankalin jama’a a bikin na 2024.

Tsohuwar uwargidan ta zauna tare da sauran manyan baki inda ta yi kallo da sauraron raye-raye masu ban sha’awa daga ƙungiyoyin da suka fafata.

Aisha Buhari
Aisha Buhari da sauran baki na kallon bikin al'adun Kalaba na 2024. Hoto: El-Masjid Abdul Umar
Asali: Facebook

Taken bikin Kalaba ya ja hankalin duniya

Business Day ta wallafa cewa gwamnan Jihar Cross River, Bassey Otu, ya bayyana cewa taken bikin na bana ya dace da ci gaba da haɗin kai a duniya.

Gwamna Bassey Otu ya ce suna buƙatar samar da tattalin arziki, zamantakewa, da ci gaban al’adu domin amfanin jama'ar jihar a dalilin bikin.

An shafe shekaru ana bikin al'adun Kalaba

Gwamna Otu ya yaba wa tsofaffin gwamnonin jihar, Donald Duke, Liyel Imoke, da Farfesa Ben Ayade, saboda ƙoƙarinsu wajen farawa da kuma ci gaba da bikin.

Kara karanta wannan

2027: Ana zargin Gwamna da balle hotunan sanata da rikicin APC ya kazanta

Bikin al'adun Kalaba wanda aka fara tun a shekarar 2004, ya shafe shekaru sama da 10 yana jan hankalin jama’a daga dukkan sassan duniya.

Fatima Buhari ta zamo jadakar ANAN

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar ANAN ta nada 'yar tsohon shugaban kasa, Fatima Muhammadu Buhari a matsayin jakada.

Rahotanni na nuni da cewa Fatima Muhammadu Buhari jakada ne bayan an zabe ta jagorantar kungiyar mata ta PROWAN a jihar Katsina.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng