Tinubu Ya Tura Sako Mai Muhimmanci Ga Mai Dakin Buhari, Ya Fadi Halayenta

Tinubu Ya Tura Sako Mai Muhimmanci Ga Mai Dakin Buhari, Ya Fadi Halayenta

  • Mai dakin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ta gudanar da bikin ranar zagayowar haihuwarta a yau Asabar 17 ga watan Faburairu
  • Shugaban kasa, Bola Tinubu ya taya mai dakin Buhari, Aisha Buhari kan bikin ranar haihuwar tata inda ya ce jaruma ce mai kishin al’umma
  • Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin shugaban, Ajuri Ngelale ya fitar a yau Asabar 17 ga watan Faburairu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Shugaban kasa, Bola Tinubu ya tura sakon murna ga matar tsohon shuaban kasa, Muhammadu Buhari.

Tinubu ya tura sakon murnar ce don taya Aisha Buhari murnar zagayowar ranar haihuwarta shekaru 53.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya samu babban mukami, kungiyar AU ta ba shi nauyi a nahiyar Afrika

Tinubu ya taya mai dakin tsohon shugaban kasa murna
Tinubu ya taya Aisha Buhari murnar zagayowar ranar haihuwa. Hoto: Bola Tinubu, Aisha Buhari.
Asali: Facebook

Wane sako Tinubu ya aike ga Aisha Buhari?

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin shugaban, Ajuri Ngelale ya fitar a yau Asabar 17 ga watan Faburairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban ya ce Aisha ta kasance mai himma wurin ayyukan alkairi da za su taimaki al’umma.

Sanarwar ta ce:

“Shugaba Bola Tinubu ya na taya Aisha Buhari, uwar dakin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari murna kan bikin ranar haihuwarta.
“Shugaba Tinubu ya taya ya Aisha ne murnar ganin yadda ta himmatu wurin aiwatar da ayyukan alkairi ba tare da son kai ba.
“Tinubu ya yabawa Hajiya Aisha Buhari ganin yadda ta ke taimakawa al’umma da marasa karfi.”

Tinubu ya godewa Aisha Buhari

Sanarwar ta kara da cewa:

“Tinubu ya godewa Hajiya Aisha Buhari da iyalanta kan irin gudunmawa da goyon baya da suke ba shi.”

Kara karanta wannan

"Sun rasa muryarsu karkashin Buhari": Shehu Sani ya magantu yayin da sarakunan Arewa ke sukar Tinubu

A karshe, Tinubu ya yi wa Aisha Buhari fatan samun rayuwa mai inganci da ci gaba a shekarun gaba.

Buhari ya tura sakon jaje

A baya, kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya tura sakon jaje ga al’ummar Yobe kan rasuwar Abba Ibrahim.

Tsohon gwamnan jihar Yobe, Sanata Bukar Abba ya rasu ne a Saudiyya bayan ya sha fama da jinya na tsawon lokaci.

Buhari ya ce tabbas ya yi babban rashin aboki wanda ya himmatu wurin tabbatar da ci gaban al’umma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel