Mata da Miji da 'Ya'yansu Sun Kone Kurmus a Bom din da Jirgi Ya Saka a Sokoto

Mata da Miji da 'Ya'yansu Sun Kone Kurmus a Bom din da Jirgi Ya Saka a Sokoto

  • Al'ummar jihar Sokoto na cigaba da bayar da labarin yadda wani jirgin soji ya saki boma bomai a kan wasu mutane a wasu kauyuka
  • Wata mata ta bayyana yadda ta rasa iyayenta da ‘yan uwanta a harin da jirgin ya kai a karamar hukumar Silame ta jihar Sokoto
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa harin ya yi sanadin mutuwar mutane 10, jikkata da dama da kuma lalata dukiyoyi masu yawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Sokoto - Ana cigaba da samun bayanai daga wajen al'umma da jami'an tsaro kan boma bomai da jirgin soji ya saka a wasu yankunan Sokoto.

Wata mata da ta tsira daga harin da ya faru a ƙaramar hukumar Silame ta bayyana mawuyacin hali da ta shiga.

Kara karanta wannan

NAF: Rundunar sojin sama ta yi magana kan rahoton kuskuren kashe bayin Allah a Sokoto

Jirgin yaki
Harin Sokoto ya hallaka mata da miji. Hoto: Giang Huy
Asali: Facebook

A wata hira da aka wallafa a BBC Hausa, matar ta ce iyalanta sun tafka asarar rayuka da kuma dukiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mata da miji da 'ya'yansu suka kone

Wata mata da ta tsallake rijiya ta baya a harin ta bayyana cikin kuka cewa ta rasa mahaifinta, mahaifiyarta, da ‘yan uwanta maza guda uku a harin.

Daily Trust ta rahoto cewa matar ta kara da cewa ta ga mahaifiyarta, mahaifinta, da ‘yan uwanta suna konewa a cikin wuta amma babu yadda za ta yi wajen ceto su.

Wani mazaunin yankin, Usman Manuga, ya bayyana cewa bayan sallar Asuba suka ga jiragen sama suna shawagi. Ba da jimawa ba, aka fara saukar da boma-bomai.

Sojoji sun yi alƙawarin bincike kan lamarin

Kakakin rundunar sojin sama, Air Vice Marshal Olusola Akinboyewa, ya tabbatar da cewa harin ya gudana ne ne kan sahihan bayanai daga kafofi masu yawa.

Ya ce za su gudanar da cikakken bincike kan rahotannin da ke nuna cewa harin ya shafi fararen hula, kuma za su sanar da jama’a sakamakon binciken.

Kara karanta wannan

"Tsoron yin aure nake yi': Jarumar fina finai ta fadi gaskiya kan rayuwarta

An kama gawurtaccen dan daba a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa 'yan sandan jihar Kano sun kama wani kasurgumin dan daba da aka fi sani da Awu.

Legit ta wallafa cewa ana zargin matashin ne da haddasa rikicin daba a unguwannin jihar Kano kuma ya amince da laifinsa yayin bincike.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng