Akwai Matsala: An Yi Hasashen Dala Za Ta Kai N4000 Kafin Karshen 2024, An Fadi Dalili

Akwai Matsala: An Yi Hasashen Dala Za Ta Kai N4000 Kafin Karshen 2024, An Fadi Dalili

  • An yi hasashen darajar Naira ta Najeriya za ta yi ƙasa warwas zuwa N4000/$1 kafin ƙarshen shekarar 2024
  • A yayin wata hira, shahararren lauyan Najeriya Mike Ozekhome ya yi wannan hasashen a ranar Talata 27 ga watan Fabrairu
  • Babban Lauyan ya ce ya ji takaicin yadda wasu mutanen da ke zaune a ƙarƙashin bishiya suka riƙe tattalin arziƙin Najeriya domin azurta kansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Mai rajin kare haƙƙin bil’adama Mike Ozekhome ya yi hasashen cewa idan har Naira ta ci gaba da faɗuwa idan aka kwatanta da Dala a halin yanzu, farashin canji zai kai N4000 nan da ƙarshen shekarar 2024.

Ozekhome ya bayyana haka ne a wata hira da gidan talabijin na Channels tv a ranar Talata, 28 ga watan Fabrairu, inda ya bayyana damuwarsa da cewa babu wata alama da ke nuni da dakatar da faɗuwar darajar Naira.

Kara karanta wannan

Sabon gwamnan CBN da tawagarsa ne suka jefa ƴan Najeriya cikin tsadar rayuwa? Gaskiya ta fito

Ozekhome ya yi hasashen faduwar Naira
Ozekhome ya hasaso faduwar darajar Naira Hoto: Mike Ozekhome, Getty Images
Asali: UGC

A kalamansa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A yau, mun biya wasu dala miliyan 400 da aka gano. Dangane da kuɗaɗen da ke asusun ajiya, ya haura dala biliyan 34.
"Idan ba mu yi taka-tsan-tsan ba, za mu kai ga halin da ake ciki a Ghana, inda suke ɗaukar Cedi a cikin kwanduna zuwa kasuwa domin su je su sayo abin da za su sanya a aljihunsu."
"Me yasa wasu tsirarun ƴan canji da ke a ƙarƙashin bishiyoyi da tebura ke sarrafa tattalin arziƙinmu."

Ozekhome ya jaddada muhimmancin gwamnati ta dauki ƙwararan matakai domin sauƙaƙa wahalhalun da jama'a ke fuskanta, inda ya ba da shawarar komawa kan muhimman tsare-tsare da dabaru.

Yadda Tinubu, APC suka yi kuskure – Ozekhome

Ya kuma bayyana mamakinsa dangane da yadda gwamnati mai ci ke danganta ƙalubalen tattalin arziƙin kasa ga gwamnatocin baya kawai.

Babban Lauyan ya ce:

Kara karanta wannan

Su wanene suka cancanci tallafin N25,000 duk wata na gwamnatin tarayya da yadda za a samu?

"Amma a wurina, abin kunya ne idan na ga jami’an wannan gwamnati suna zargin gwamnatin Jonathan da ta bar mulki a 2015, kusan shekaru 10 da suka wuce.
"Wani abin ban mamaki har ɗora laifi yake a kan magabacinsa da suka karɓi mulki a gwamnatin APC. Ina tunanin komai ya lalace."

Ozekhome ya yi nuni da cewa alƙawarin da gwamnatin yanzu ta yi na sabunta fata ya koma matsalar tattalin arziƙi.

A kalamansa:

"Wannan ba sabunta fata bane, wannan sabon talauci ne."

CBN Ya Ɗauki Matakin Farfaɗo da Darajar Naira

A wani labarin kuma, kun ji cewa babban bankin Najeriya ya ɗauki matakin farfaɗo da darajar Naira wacce ta faɗi ƙasa warwas.

Bankin na CBN ya dawo da sayar da Dala ga masu harkar cinikin kuɗaɗen ƙasashen waje da ake kira da BDC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel