Sabon Gwamnan CBN da Tawagarsa Ne Suka Jefa Ƴan Najeriya Cikin Tsadar Rayuwa? Gaskiya Ta Fito

Sabon Gwamnan CBN da Tawagarsa Ne Suka Jefa Ƴan Najeriya Cikin Tsadar Rayuwa? Gaskiya Ta Fito

  • Gwamnan CBN ya nesanta kansa daga hannu a jefa ƴan Najeriya cikin wannan halin na yunwa da matsin tattalin arziki
  • Olayemi Cardoso ya bayyana cewa shi da tawagarsa ba su suka jawo tsadar rayuwa ba, amma zasu yi duk mai yiwuwa don shawo kan komai
  • Ya faɗi haka ne yayin da yake jawabi jim kaɗan bayan kammala taron kwamitin MPC karo na farko karkashin jagorancinsa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Olayemi Cardoso, ya nesanta kansa daga zama sababin halin kuncin da 'yan Najeriya ke ciki a halin yanzu.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ‘yan Najeriya sun koka kan halin matsin tattalin arzikin da kasar ke ciki sakamakin tsare-tsaren da gwamnati ta ɓullo da su da sunan garambawul.

Kara karanta wannan

"A shigo da abinci" TUC ta gano hanya 1 da zata share hawayen talakawa, ta aike da saƙo ga Tinubu

Gwamnan CBN ya nesanta kanda daga zargin halin da ake ciki.
Gwamnan CBN Cardoso: Banai da hannu a halin ƙuncin da yan Najeriya ke ciki Hoto: CBN
Asali: Twitter

Tun a watan Mayu, 2023 a wurin bikin rantsar da shi, shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya sanar da kudurinsa na yin sauye-sauye, inda nan take ya tabbatar da tuge tallafin man fetur.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan haka kuma shugaban ƙasar ya kuma ɗauki matakin zare hannun gwamnati a hada-hadar kudin Najeriya watau Naira, PM News ta rahoto.

CBN ne ya jawo halin matsin da ake ciki a Najeriya?

Da yake jawabi ranar Talata a taron farko na kwamitin kula da harkokin kudi (MPC) karkashin jagorancinsa, Cardoso ya ce ba shi da hannu a jefa kasar cikin ƙaƙanikayi.

Gwamnan babban bankin Najeriya, Cardoso ya ce shi da tawagarsa ba su da hannu a matsalolin tattalin arzikin da ‘yan Najeriya ke fuskanta.

Ya ba da tabbacin cewa babban bankin na daukar matakan da suka dace don ganin an dawo da harkokin kudi kan turba, kamar yadda yake a baya.

Kara karanta wannan

Murna yayin da gwamnatin Tinubu ta shirya rabon tallafin N25,000 ga 'yan Najeriya

Da yake amsa tambaya kan ko manufofin da CBN ya bullo da shi a karkashinsa ne ya jefa ƙasar nan cikin wannan hali, Cardoso ya ce:

"Wannan tambayar abun dariya ce amma ya kamata ƴan Najeriya su sani gwamnan CBN, ni da tawaga ta bamu muka jefa su cikin tsadar rayuwar nan ba, mu wani ɓangare ne na hanyar warware komai.
"Mun kuduri aniyar zamu yi aiki tukuru domin ganin mun tsamo ƙasar nan daga cikin halin da take ciki."

Menyasa NLC ta ɓarke da zanga-zanga?

A wani rahoton kuma Ƴan kwadago sun bayyana cewa babban dalilin wannan zanga-zanga da mambobi suka fito shi ne yunwar da ƴan kasa ke ciki.

Joe Ajaero ya ce batun mafi ƙarancin albashi abin dubawa ne amma ba shi ne asalin abinda ya haddasa NLC fara zanga-zangar kwana biyu ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel