Jerin Kasashen Duniya 5 Da Ya Kamata Ka Ziyarta Kafin Su Kara Yawan Jama’a

Jerin Kasashen Duniya 5 Da Ya Kamata Ka Ziyarta Kafin Su Kara Yawan Jama’a

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Yayin da mutane ke kara fadada sanayyarsu da duniya, ƴan Afirka, Asiyawa, Turawa, da Amurkawa sun binciko wuraren yawon bude ido daban-daban.

A yanzu masu sha'awar yawon bude ido a duniya na bincike kan wuraren da ba a taba zuwa ba da kuma wadanda ke da ingantattun al'adu don debe kewa.

Kasashen zuwa yawon bude ido
Jerin kasashe 5 da ya kamata ka ziyarta a 2024
Asali: Getty Images

A cikin wannan labarin, akwai jerin kasashe biyar masu tsari kuma masu kyan gani don ziyarta kafin shekarar 2024 ta wuce, Vanguard ta ruwaito.

Wadannan kasashe suna ba da wani nau'i na musamman na kyawawan dabi'u, wadatar al'adu, bude ido, kafin 'yan cirani su yi masu yawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Bayan shafe kusan mako a hannun 'yan bindiga, dalibai da malaman makaranta sun shaki iskar 'yanci

1. Jojiya

Kasar Jojiya
Kasar Jojiya na da kololuwar dusar kankara da rairayin teku. Hoto: Steve Kelley
Asali: Getty Images

Jojiya ta kasance kasa mai wurare na ban sha'awa, tun daga kololuwar dusar ƙanƙara na tsaunin Caucasus zuwa rairayin bakin teku mai jan hankali.

Jojiya tana tsakanin Turai da Asiya, tare da Tbilisi a matsayin babban birnin kasar, kuma tana da gine-ginen tarihi, kasuwanni da al'umma mai cike da fasaha.

2. Bhutan

Kasar Bhutan
Kasar Bhutan na da gine-gine masu ban sha'awa. Hoto: Holly Wilmeth
Asali: Getty Images

Bhutan wata boyayyiyar alkarya ce da ke gabashin Himalayas, kuma ta kasance matattarar masu yawon shakatawa na tsawon zamani.

Ba da fifiko ga ma'aunin farin ciki na kasa sama da GDP, wannan kasa tana ba da bambance-bambancen kyawawan al'adun gargajiya da gine-gine masu ban sha'awa.

3. Madagaska

Madagascar
Madagaska ta na da tsirrai da abubuwan al'ajabi. Hoto: Yann Guichaoua
Asali: Getty Images

Madagaska ta kasance kamar wata aljannar duniya ga masu son tsirrai da abubuwan al'ajabi. Tana da yanayi wanda ke kara wa kasar yawan masu zuwa yawon bude ido.

Yayin da kuka nishadantu da ganin rukunin bishiyoyin Kuka na tarihihi, a hannu daya akwai dajin Andasibe-Mantadia, mai dauke da namun daji kala-kala.

Kara karanta wannan

Karin farashin fulawa: Masu yin Gurasa a Kano sun gudanar da zanga-zanga

4. Oman

Kasar Oman
Kasar Oman ta zamo mafaka a yankin Larabawa. Hoto: Sanniely
Asali: Getty Images

Yayin da al'ummomin da ke kusa da su ke jawo dimbin yan yawon bude ido, Oman ta zamo kasar da ke ba da mafaka a yankin Larabawa.

Za ku hadu da karimcin mutanen Omani, musamman idan kuka shiga cikin birnin Nizwa mai tarihi, ga abubuwan al'ajabi na gine-gine na Muscat.

5. Sri Lanka

Sri Lanka
Kasar Sri Lanka na da bishiyoyin shayi. Hoto: Shakeel Sha
Asali: Getty Images

Duk da karuwar shahararta a baya-bayan nan, Sri Lanka har yanzu tana riƙe da kambunta na karrama baki.

Ƙasar tsibirin tana da shimfidar kasa mai ban sha'awa, daga shukar bishiyoyin shayi zuwa rairayin bakin teku na zinari da kuma kanguna na tarihi.

Bude idonka ta hanyar ziyartar tarihin Sigiriya, da ziyartar gandun dabbobi na Yala, kuma ku ɗanɗana gardin ganyen shayin Ceylon.

Jerin kasashen duniya da rana ba ta faduwa

A wani rahoton makamancin wannan, Legit Hausa ta tattaro bayani kan wasu garuruwa da ke cikin kasashen duniya wadanda rana ba ta faduwa.

Yi nazarin wadannan kasashen a wannan likau din.

Asali: Legit.ng

Online view pixel