Mutumin Da Ya Rasa Aikinsa Ya Saki Matansa 3 A Rana Daya Bayan Sun Fara Cin Amanarsa

Mutumin Da Ya Rasa Aikinsa Ya Saki Matansa 3 A Rana Daya Bayan Sun Fara Cin Amanarsa

  • Wani mutum mai suna Mutiacya ya sake matansa uku gaba daya a rana daya bayan sun ci amanar shi a zaman aure
  • Mutumin mai shekaru 55 ya ce a lokacin da ya ke da hali babu abinda matan suka nema suka rasa kuma su na kaunar shi sosai
  • Ya ce daga bisani bayan rasa aikinsa sai duka su ka fara bin wasu maza masu kudi tare da cin amanar shi a ko wane lokaci

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani mutum dan kasar Uganda da ke da mata uku ya wayi gari da zaman kadaici bayan ya rabu da dukkan matan nasa.

Mutiacya wanda ya auri kyawawan mata ya ce ya rabu da su ne a rana daya bayan sun kuntata masa da kuma cin amana, Legit.ng ta tattaro.

Wani ya sake matansa 3 a rana daya bayan sun ci amanarsa a Uganda
Mutumin Ya Bayyana Yadda Ya Yi Dawainiya Da Su Kafin Rasa Aikinsa. Hoto: Afrimax English.
Asali: UGC

Yayin da ya ke hira da Afrimax English, mutumin mai shekaru 55 ya ce a baya matan nasa sun kasance masu kan-kan da kai kuma ga tarbiya.

Kara karanta wannan

Karen Mota Ya Yi Karambani da Tirelar Dangote, Ya Ɓurma Gida Ya Murƙushe Yara

Mutumin ya bayyana yadda ya yi dawainiyar matan a baya

A cewarsa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“A baya suna da kokarin ganin sun gina iyalina, amma daga baya sun fara nuna wasu halaye da ba zan iya dauka ba.
“Na dauki matakin korarsu ba a son raina ba amma kuma ya zama dole kuma ya dace.”

An haifi Mutiacya a kasar Chadi amma ya na rayuwa a Uganda inda ya shafe fiye da shekaru 34 a kasar.

Ya ce babu abin da matan nan suka nema suka rasa a wurin shi saboda irin kulawa da ya ke ba su gaba daya.

Amma daga bisani bayan ya rasa aikin shi yadda ba ya iya daukar dawainiyarsu kamar a baya, wanna shi ne silar samun matsalarsu.

Ya ce sun fara cin amanar shi inda suke bin maza masu kudi

Kara karanta wannan

Abubuwa 4 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Mutumin Da Ya Kashe Sama Da Miliyan 10.7 Don Ya Zama Kare

Ya ce:

“Lokacin da na ke aiki, matan nan duka suna kaunata saboda suna samun komai na rayuwa, bayan rasa aikina dukkansu sun yaudare ni.
“Abin haushi shi ne yadda suke cin amana ta wurin bin ma su kudi, ni kuma na ga ba zan iya daukar wannan bakin ciki ba, sai na kore su a rana daya.”

Tun daga ranar, Mutiacya ya manta da maganan aure ya shiga harkar taimakon al’umma musamman yara kanana.

Ya ce ya na jin dadi yadda ya ke taimakon marasa karfi saboda hakan na saka masa farin ciki tare da mantar da shi abin da ya faru.

Miji Ya Yi Barazanar Sake Matarsa Saboda Ta Ki Daukar Ciki, Ya Sha Suka Daga Mutane

A wani labarin, wani mutum dan Najeriya ya yi barazanar sakin matarsa bayan ta ki amincewa ta sa ke haihuwa da shi.

Mutumin ya ce yanzu haka su na da 'ya'ya hudu da matar amma ta ce ita kam ba za ta sa ke haihuwa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel