Rikita-Rikita Yayin Da Miji Ya Yi Barazanar Sakin Matarsa Saboda Ta Ki Daukar Ciki, Mutane Sun Caccake Shi

Rikita-Rikita Yayin Da Miji Ya Yi Barazanar Sakin Matarsa Saboda Ta Ki Daukar Ciki, Mutane Sun Caccake Shi

  • RIkita-rikita yayin da wani dan Najeriya ya yi barazanar sakin matarsa da suka haifi ‘ya’ya hudu
  • Mutumin na zargin matar da shan kwayoyin hana daukar ciki bayan ta ki haifa masa da na biyar
  • Mutane da dama sun mai da martini inda mafi yawa suke kushe wannan hali na mutumin

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani dan Najeriya ya yi barazanar sakin matarsa saboda kin amincewa da kara haihuwa da shi.

Mutumin ya ce matar tasa bayan ta haifi ‘ya’ya hudu ta ce ba za ta sake haihuwar da na biyar ba, cewar Legit.ng.

Miji Ya Yi Barazanar Sakin Matarsa Saboda Ta Ki Daukar Ciki Don Ta Haifu
Miji Ya Yi Barazanar Sakin Matar Ne Bayan Ya Na Zargin Ta Na Shan Kwayoyin Hana Daukar Ciki. Hoto: Peeterv, Commerce and culture stock.
Asali: Getty Images

Wani mai amfani da kafar sada zumunta ta Facebook, Imaan Mike Umoh shi ya wallafa hakan inda ya ce abin ya faru a layin unguwarsu.

Mijin na zargin matar da shan magani don hana daukar ciki

Kara karanta wannan

Radadin Cire Tallafi: Martanin 'Yan Najeriya Kan Aniyar Tinubu Na Raba N8000 Ga Gidaje 12m

Ya ce mijin na zargin matar ta na shan kwayoyi don hana ta daukar ciki wanda yanzu haka suna da ‘ya’ya hudu da matar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mike ya wallafa kamar haka:

“Da dumu-duminta.
“Gagarumar fada a layin unguwan mu.”
”Miji ya yi barazanar sakin matarsa idan ta ki amincewa ta dauki cikin dan su na biyar.
“Ya na zargin matar tasa da shan kwayoyi don hana daukar ciki bayan ta haifa masa yara hudu.”

Mutane sun caccaki mijin kan wannan hukunci

Wallafawar ta jawo martanin mutane da dama yayin da suka fadi ra’ayinsu a

kan hakan.

Mag Love:

“Wannan ai da sauki ma yara 5, makwabci na matarsa ta haifa masa ‘ya’ya tara kuma babu abincin kirki, da ba ta haihu ba har shekaru biyu, mijin kawai ya yi zargin cewa ta na shan kwayoyin hana daukar ciki.”

Kara karanta wannan

Kwanaki 42 Akan Mulki, Gwamnatin Tinubu Ta Gagara Cika Babban Alkawari Da Ta Dauka Wa Yan Najeriya

Etiime Idiong:

“A yanzu haihuwar yara da yawa hatsari ne, don a karshe shaidan zai zabi daya da zai dame ku har karshen rayuwarku.”

Promise William:

“Idan ya biya sadaki kuma ya na iya daukar nauyinsu, ba damuwa ba ne idan matar ta kara haihuwa.”

Love Sylvanus Nse:

“Wannan mutumin har yanzu bacci ya ke yi, ku ce masa ya tashi har yanzu muna Najeriya ne ba mu koma Algeria ba.”

Akpan Idongesit:

“Ta bashi mana. Hakkinsa ne.”
“Babu wanda zai tambaye shi ta yaya ko meyasa.
“Mutane sun bambanta da juna.”

Ubongabasi Ikpe:

“Idan za ka yi bincike sosai babu isasshen abinci a gidan amma kuma ya na son karin haihuwa, ya yi ciki ya haifa da kansa mana.”

Blessed Okon Imoh:

“Bayan karin farashin kaya, babu wanda ya ke duba lafiyar ita mai daukar ciki, ko kuma hatsarin da ke ciki, maza suna tunanin daukar ciki sauki ne.”

Kara karanta wannan

Innalillahi: Motar da ta dauko masu zuwa 'party' ta yi karo da motar yashi, mutum 20 sun mutu

"Muna Ji A Jikinmu": Budurwa Ta Koka Kan Karancin Samari

A wani labarin, wata budurwa da ke rayuwa a Germany ta koka kan yadda suke shan wahala a neman samari.

Budurwar ta wallafa wani faifan bidiyo inda ta ce ‘yan mata a Germany sai sun biya kudi samari suke zuwa musu hira.

Ta ce idan kina son saurayi ya zo miki hira dole za ki biya kudin sufuri da kuma abincin da zai ci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel