"Ya Yi Bulokin Dina": Budurwa Ta Koka Bayan Saurayinta Ya Dandana Abincinta Ya Tsere, Ta Tambayi Dalili

"Ya Yi Bulokin Dina": Budurwa Ta Koka Bayan Saurayinta Ya Dandana Abincinta Ya Tsere, Ta Tambayi Dalili

  • Budurwa ta wallafa wani hoto na hadadden abinci da ta yi wa saurayinta ya jawo cece-kuce a kafar sada zumunta
  • Budurwar mai suna @literally_rae ta wallafa hoton inda ta ce tayi mamakin yadda saurayin nata ya katange ta daga dukkan kafafen sada zumunta
  • Ta ce bayan saurayin nata ya dandana abincin, daga nan bata sake jin duriyar sa ba, ta nemi jin me hakan ke nufi a shafin ta na Twitter

Wata budurwa mai suna @literally_rae ta wallafa wani hoton hadadden dafa-duka da ta yi wa saurayinta.

Ta bayyana bakin cikinta yadda saurayin nata ya bar daukar wayanta kwana daya da dandana abincin.

Budurwar yayin da take kuka akan saurayin nata bayan dandana abincin
Budurwa Ta Koka Bayan Saurayinta Ya Dandana Abincinta. Hoto: Literally_rae/ Twitter, Andrew Lichtenstein/ Getty images.
Asali: UGC

Hoton hadadden abincin na dauke ke da shinkafa da zuka-zukan kifi guda biyu.

Yayin da take yada hoton, ta rubuta a sama kamar haka:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Amarya Da Ango Sun Keta Daji a Kafa Zuwa Wajen Daurin Aurensu, Bidiyonsu Ya Yadu

"Na hada wannan abinci na musamman ga saurayina, amma kwana daya ya katangeni ba na iya samunsa a waya, ko akwai wani matsala?"

Ta kara da cewa, ta hadu da shi ne a kafar sadarwa ta Twitter amma ya katangeta a dukkan kafafen sadarwa.

Ga hoton da ta wallafa:

Mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu, kamar yadda Legit.ng ta tattaro.

Wasu sun yi tsokaci tare da tausaya mata, yayin da wasu suka caccake ta da cewa ta gama wahala amma ya gudu.

Yayin da wasu suka ce abincin ta ne bai yi dadi ba, kuma ya yi abin da ya dace.

Martanin mutane da dama a kafar sada zumunta:

@hardeydoying:

"Gumaka ba sa karbar sadaukarwa rabi, ina dafaffen kwai?"

@MAYOR_....:

"Yunwa bai ci karfinsa ba ne, da ba zai yi wasa da abinci ba."

STARBOY RICHEE O*O:

"Wannan kwamachalar shinkafar, da kin saka dafaffen kwai."

Kara karanta wannan

"Sai Da Ya Yi Hawaye": Matashiya Ta Ba Direba Mai Kirki N10,000 Bayan Ya Caje Ta N2,500 Duk Da Tsadar Mai

@fuzzyna22:

"Bayan ya baki 50k don abinci, kin dafa wannan."

@LionStarzy:

"Karya ne, ki nuna mana shaidan ya katange ki, kuma watakila masanin ganyayyaki ne idan labarin ki gaskiya ne."

@ObajiStar ... :

"Abincin yana da kyau ga ido, amma bansan dandano ba."

@BEAUTYBYKI.:

"Wannan shi ne abin da nafi so, dubi kifi ohh Allah na."

@RadicalTh...:

"Ki je ki ba wa babanki idan ya yi masa, tabbas ba matsala."

@shirlen_ray:

"Wannan babu abin burgewa."

@ToonzPhil:

"Dafa dukan bata dafu duka ba."

Mata Ta Koka Bayan Siyar Da Wayarta Ta Biya Wa Mahaifiyarta Tiyata Yayin Da Attajirin Mijinta Ya Ki Taimaka Mata

A wani labarin, wata mata ta bayyana bakin cikinta yadda ta siyar da wayarta don yi wa mahaifiyarta jinya.

Matar ta ce mijinta mai hali ne amma yaki ya taimaka da ko sisin kwabo saboda mako.

Ta ce da ya gane ta siyar da wayarta ya mata barazanar sai ta dawo da wayar da ta siyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel