Bidiyon Ango Na Sharɓar Kuka a Wajen Ɗaurin Aurensa Ya Ɗauki Hankula

Bidiyon Ango Na Sharɓar Kuka a Wajen Ɗaurin Aurensa Ya Ɗauki Hankula

  • Wani bidiyo mai sosa zuciya na wani ango yana sharɓar kuka a ranar ɗaurin auren sa yayin da amayar sa ke tahowa ya ɗauki hankula
  • Angon wanda yayi shiga mai ɗan karen kyau yana tsaye ne yana jiran zuwan amaryar sa yayin da hannayen sa sune ta kakkarwa
  • Daga cikin abokan ango yana riƙe da shi domin kwantar masa da hankali yayin da yake ta sharɓar kuka abin sa

A cikin ƴan kwanakin nan ana yawan sanya bidiyoyin anguna waɗanda ke sharɓar kuka da sun hango amaren su na tahowa a ranar ɗaurin auren su.

A cikin ɗaya daga cikin irin waɗannan bidiyoyin, wani sabon ango ya kasa ɓoye yadda yake ji game da auren sa inda bai ji kunya ba kawai yayi ta sharɓar kuka.

Kara karanta wannan

"Ku Riƙa Duba Litattafan Yara": Wata Mata Ta Saki Hotunan da Ta Gani a Littafin Karamin Yaro

Ango da Amarya
Bidiyon Ango Na Sharɓar Kuka a Wajen Ɗaurin Auren Sa Ya Ɗauki Hankula Hoto: TikTok/@ladygagajp
Asali: UGC

Yana tsaye a wajen ɗaurin auren sanye da wasu baƙaƙen kaya ga kuma fulawoyi riƙe a hannun sa.

Abokan sa duk sun yi shiga irin wacce yayi. A cikin bidiyon ɗaya daga cikin abokan sa ya kwantar da hankalin ango wanda yake ta shafa hannayen sa yayin da yake sharɓar kuka.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Babban abokin angon ya sanya hannun sa a bayan angon yana cigaba da kwantar masa da hankali.

Bidiyon shafin @lady_gagajp ne ya sanya shi a TikTok, inda ya rubuta a ƙasan shi cewa:

"Sai kace ba zai taɓa cin amanar ta ba."

Bidiyon ya ɗauki hankula sosai

Bidiyon ya ɗauki hankula sosai inda mutane da dama suka yi ta yin sharhi a kansa.

Ga kaɗan daga ciki:

@collymwendwa ya rubuta:

"Na haƙura. Ba zaku bar shi yayi basajar shi cikin natsuwa ba."

Kara karanta wannan

Hoto: Dalibin Sakandire Ya Zana Ƙayatacciyar N200 da Fensir Mai Kaloli, Ya Kamata CBN Ya Masa Abu 1

@p.ngqondo ta rubuta:

"Yana kuka ne kawai domin ga san ɓa zai ci amana ta sauƙi ba."

@favourzenia ta rubuta:

"Da farko na ɗauka cewa wata lallura gare shi."

Abin Mamaki: Bidiyon Yadda Wata Budurwa Ke Sarrafa Ƙafafun Ta Ya Ɗauki Hankula Sosai

A wani labarin kuma, wata budurwa mara hannuwa ta ɗauki hankula sosai a yanar gizo.

Budurwar tayi amfani da ƙafar ta wajen yin wani abu da ya ɗauki hankulan mutane sosai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel