Matashi Mai Samun N100k Ya Bukaci Budurwa Mai Samun N34m Ta Aje Aikinta Ta Aure Shi

Matashi Mai Samun N100k Ya Bukaci Budurwa Mai Samun N34m Ta Aje Aikinta Ta Aure Shi

  • Wata matashiya ƴar Najeriya ta bayyana yadda ta kaya tsakaninta da wani matashi wanda ya ke son ya aure ta
  • Budurwar ta bayyana cewa matashin yana samun N100k zuwa N200k a shekara yayin da ita kuma ta ke samun N34m
  • Sai dai ya haƙiƙance cewa bai ji daɗi ba tana samun abinda ya fi na shi inda ya buƙace ta da ta yi murabus saboda ƙauna

Mutane da dama sun caccaki wani matashi ɗan Najeriya a yanar gizo, bayan ya buƙaci budurwarsa da ta ajiye aikin da ta ke yi saboda shi.

Matashin wanda ya ke samun kusan N100,000 zuwa N200,000 a matsayin albashinsa, ya bayyana cewa baya son budurwarsa ta fi shi samu.

Matashi ya bukaci budurwarsa ta aje aiki ya aureta
Albashinta ya fi na shi sosai Hoto: @Rapideye, Carrastock
Asali: Getty Images

Ya nemi aurenta inda ya bata umarnin da ta ajiye aikinta wanda ta ke samun N34m a shekara domin su kasance tare.

Ta ki amsa tayin da ya yi mata

Cikin ruwan sanyi ta gaya masa cewa ba za ta iya yin hakan ba, amma sai ya fusata inda ya yi mata barazanar zai gayawa iyayenta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

RejiYates ta rubuta:

"Akwai wani gaye ɗan Najeriya da ya san iyayena sannan ya tambaye ni idan ba matsala zai yi magana da su domin ya nemi aurena. Sai na ce aa bani da ra'ayin auren shi."
"Ya tambayi ko meyasa na ce masa ina da dalilai na. Ya mayar da hankali kan dalilan da suka shafi batun kuɗi. Na gaya masa cewa kaurin aljihunmu ba ɗaya bane kuma bana tunanin hakan zai yi mana daɗi."
"Na ɗaya bana son na rage yanayin da na ke gudanar da rayuwata sannan kada ya matsa wa kansa dole sai samunsa ya ƙaru. Ya buƙaci ko zan iya haƙura da aikina saboda ƙauna inda na ce masa ko da wasa ba zan yi hakan ba.

"Ya gayamin abinda ya ke samu a shekara ya kai tsakanin 100,000 - 200,000, wanda ba matsala hakan. Abinda ya ke samu kenan kuma ya fiye masa."
"Na gaya masa nawa yana kai tsakanin N28m zuwa 34m, sai ya ce bai kamata ina samun abinda ya fi na saurayina ba."
"Na gaya masa cewa bai yarda da kansa inda ya ce namiji yakamata ace yana nemowa babu wani maganar rashin yarda da kai. Sai na ce masa ya je ya nemi daidai da shi ba zai iya kula da ni ba, sai kawai ya ce zai kai ƙarata wajen iyayena."
"Ni ban damu ba idan ya kai ƙara ta saboda na san iyayena tabbas dariya za su yi masa. Wannan tunanin na shi ma ai hauka ne. Meyasa ba zan iya samun abinda ya fi na shi ba, sannan meyasa zan ƙyale wannan albashin da aikin? Ya ce matan yanzu so suke su zama kamar maza. Wai dama haka matan Najeriya ke fama?"

Bafulatana Ta Bayyana Aniyarta Ta Yin Wuff Da Inyamuri

A wani labarin na daban kuma wata kyakkyawar budurwa Bafulatana ta bayyana burinta na yin wuff da Inyamuri.

Bafulatanar wacce tsatsonta ƴan asalin jihar Kano ne tace ta daɗe da wannan burin a zuciyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel