Wani Matashi Ya Kwato Soyayyar Wata Kyakkyawar Budurwa Mai Tsananin Son Saurayinta

Wani Matashi Ya Kwato Soyayyar Wata Kyakkyawar Budurwa Mai Tsananin Son Saurayinta

  • Wani matashi ɗan Najeriya ya haɗu da wata budurwa a Facebook wacce ke matuƙar son saurayin da suke soyayya tare
  • Cikin wasa matashin ya nemi da ta ba shi rabin damar da ta ba saurayinta domin nuna mata cewa ya fi shi cancanta
  • Kyakkyawar budurwar ta ba shi wannan damar inda daga ƙarshe suka tsunduma soyayya wacce har ta rikiɗe ta kai su ga aure

Wani matashi ɗan Najeriya ya bayyana labarin soyayyarsa da wata budurwa da suka haɗu a Facebook, da yadda har ya samu daga ƙarshe ya aureta.

Matashin wanda ya ke amfani sunan Mai Daraja a Facebook, ya ce watarana kawai yana cikin ƴan dube-dubensa a Facebook sai ya ci karo da wata kyakkyawar budurwa mai suna Maryam.

Matashi ya yi wuff da kyakkyawar budurwa
Matashin ya nemi ta ba shi rabin damar da ta ba saurayinta Hoto: @maidaraja
Asali: Facebook

Sun fara yin magana da juna

Kara karanta wannan

"Baya Son 'Ya'ya Mata": Matar Aure Ta Garzaya Kotu Neman a Raba Auren Da Ke Tsakaninta Da Mijinta

Ya bayyana cewa ta burge shi inda ya yanke shawarar ya nemi ta zama ƙawar shi a Facebook. Ta aminta da hakan inda suka fara hira a tsakaninsu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Nan da nan kawai sai ya fahimci cewa Maryam tana da saurayi wanda ta ke kira da suna “Nisful-Hayat”, wanda ke nufin Rabin Raina.

Maryam tana alfahari da saurayin nata inda ta ke yawan ɗora hotunansa a soshiyal midiya.

Matashin ya bayyana cewa bai karaya ba duk da ya fahimci tana soyayya da wani daban, inda cikin wasa ya nemi soyayyarta. Ya ce ya yi mamaki lokacin da ta ƙi amsar tayinsa nan take, inda tace saurayinta kawai ta ke so.

Ya gaya mata cewa abinda ta yi masa bata kyauta ba yakamata ta ba wasu daban dama su jaraba sa'ar sace zuciyarta.

Ta ba shi rabin damar da ya buƙata

Kara karanta wannan

"Kadaici Ya Addabe Ni": Dirarriyar Matashiya Ta Koka a Yanar Gizo, Tana Neman Saurayi Ruwa Ajallo

Ya nemi da ta ba shi rabin damar da ta ba saurayinta indai har tana son ta yi masa adalci. Ta tambaye shi cewa ta yaya ya ke son hakan ta kasance, sai ya ce mata tunda shine rabin ranta ta ba shi dama shi ma ya zama rabin ranta.

Ta yi dariya inda ta amince da buƙatarsa. Tun daga nan suka fara kiran juna RRR inda abotarsu daga baya ta rikiɗe ta zama wani abu babba.

Sun tashi daga Facebook sun koma WhatsApp inda daga ƙarshe suka haɗu ido da ido, daga nan suka yanke shawarar su yi aure.

Dirarriyar Matashiya Ta Koka a Yanar Gizo, Tana Neman Saurayi Ruwa Ajallo

Wata dirarriyar matashiya ta garzaya yanar gizo neman saurayi bayan kaɗaicin rashin masoyi ya addabe ta.

Matashiyar tace a shirye ta ke tsaf ta amshi soyayyar wanda ya shirya amma da sharaɗin sai yana da wadata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel