Matashi Ya Ciyo Bashin N500k Daga Banki, Ya Ba Budurwarsa Ta Sha Shagalinta

Matashi Ya Ciyo Bashin N500k Daga Banki, Ya Ba Budurwarsa Ta Sha Shagalinta

  • Wata budurwa ta bayyana yadda saurayinta ya shagwaɓa ta da kyautar tsabar kuɗi har N500,000 domin ta sha shagalinta
  • Labarin ya yaɗu a Twitter saboda budurwar ta bayyana cewa saurayin na ta bashin kuɗin ya ciyo daga banki
  • Mutane da dama sun yi martani kan labarin da kalaman barkwanci, amma budurwar tace ta yi sa'ar masoyi

Wani matashi ɗan Najeriya ya gwangwaje budurwarsa da kyautar N500,000 ta sha shagalinta yadda ta ke so.

Budurwar mai amfani da sunan @praiseoghre a Twitter, ta bayyana yadda saurayin na ta ya bata kulawa inda ya bata N500k ba zato ba tsammani.

Matashi ya ciyo bashin N500k saboda budurwarsa
Matashin ya ce ta sha shagalinta Hoto: Getty Images/Yana Iskayeva, Bloomberg da Peoplesimages (An yi amfani da hotunan ne kawai)
Asali: Getty Images

Sai dai, mutane sun cika da mamaki lokacin da ta bayyana cewa saurayin na ta, ciyo bashin N500,000 ɗin ya yi daga banki.

Labarin saurayin da ya ba budurwarsa N500k ta sha shagalinta

Kara karanta wannan

Matashiya Ta Ajiye Girman Kai, Ta Isa Gaban Saurayinta Da Zobe Domin Neman Aurensa, Hotuna Sun Yadu

Praise ta bayyana cewa ta nemi saurayin na ta ne da ya nuna mata irin son da ya ke mata, inda ya je ya ciyo bashin kuɗin domin ta kashe su yadda ta ke so.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta bayyana cewa ta yi sa'ar samun saurayi irinsa wanda zai yi duk mai yiwuwa wajen ganin ya faranta mata rai.

Labarin na cewa:

"Na tambayi saurayina ya gwada min irin son da ya ke min, sai ya ciyo bashin N500k daga Palmpay, sannan ya ce min na kashe su yadda raina ya ke so, duk kuwa da cewa N40k kawai ya ke samu a wata. Ba wanda zai gaya min wani abu daban na yarda, wannan saurayin nawa yana matuƙar ƙaunata. Gaskiya na yi sa'a."

Labarin ya janyo masu amfani da Twitter sun bayyana mabanbantan ra'ayoyi, inda suka tofa albarkacin bakinsu.

Kara karanta wannan

"Ni Na Fara Cewa Ina Son Shi": Dattijuwa 'Yar Shekara 60 Mai Soyayya Da Matashi Dan Shekara 27 Ta Bayyana Irin Son Da Ta Ke Masa

Ga kaɗan daga ciki:

cyprax ya rubuta:

"Ina tunanin ba Palmpay ɗin da mu ke amfani da shi bane? 40k zuwa 500k, Palmpay ɗin da na sani ba zai yi haka ba."

@Eshious ya rubuta:

"Mutumin da ya ke samun N40k a wata, ba zai iya samun bashin N500k daga Palmpay ba."

@Abudris ya rubuta:

"Ko ba komai dai idan ƴan sanda suka zo sun tafi da ku idan ya kasa biya."

Matashi Ya Yi Wuff Da Budurwar Abokinsa

A wani labarin na daban kuma, wani matashi ya koka kan yadda abokinsa ya yiasa yankan baya ya aure masa budurwa.

Matashin ya bayyana cewa ya ɗamka amanar budurwarsa a hannun abokinsa, kawai sai suka fara soyayya wacce har ta kai su ga aure.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel