Yadda ‘Yan Sanda Suka Gano Danyen Aikin da Miyagu Ke Shiryawa Mutanen Abuja

Yadda ‘Yan Sanda Suka Gano Danyen Aikin da Miyagu Ke Shiryawa Mutanen Abuja

  • Rundunar ‘yan sandan da ke Abuja sun bada sanarwar cafke wasu mutane da suka shirin yin fashi
  • ‘Yan fashi da makamin sun yi niyyar aukawa mutanen Unguwar Apo Zone E Extension a makon nan
  • Wadanda ake zargi da tsara fashin sun tsere, amma an iya cafko wani da ake sa rai zai fallasa ragowar

Abuja - Rundunar ‘yan sandan Najeriya na reshen birnin tarayya Abuja ta fito ta ce jami’anta sun yi nasarar tono shirin da ake yi na yin fashi da makami.

A ranar Laraba, Tribune ta kawo rahoto da ya nuna cewa wasu ‘yan fashi da makami sun yi nufin yin ta’adi a Unguwar Apo Zone E Extension da ke Abuja.

A sanadiyyar haka ne aka cafke wani mutum da zargin yana da hannu a fashin da aka nemi ayi, kuma an samu abubuwan da za su zama hujja a kotu.

Kara karanta wannan

‘Yan Bindiga Sun Shiga Fada, Sun Yi Garkuwa da Basarake, An Bindige Wata Har Barzahu

Jami’in yada labarai na ‘yan sandan birnin tarayya, Josephine Adeh ya fitar da sanarwa da ta nuna sun bankado mugun nufin da ‘yan fashi suka kitsa.

SP Josephine Adeh ya fitar da jawabi

Jawabin SP Josephine Adeh ya ce da karfe 6:00 na safiyar Laraba, 12 ga watan Afrilu 2023, suka samu kira daga mutanen unguwar Apo Zone E Extension.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hakan ya sa ‘yan sandan da ke bakin aiki a shiyyar Apo suka dauki harama, nan take mutanen da ke shirye-shiryen fashin suka tsere bayan sun hango su.

'Yan sanda
Dakarun 'Yan sanda Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Rahoton Leadership ya nuna a nan miyagu su ka bar wata mota kirar BMW mai lamba ABJ 440 KX dauke da manyan talabijin uku da komfutoci biyu.

Sanarwar ta na zargin an samu kayan ne ta hanyar sata daga wasu gidaje da aka shiga.

Kara karanta wannan

Ka kama kanka: Dattawan Arewa sun ce Peter Obi na son tada hankali a Najeriiya

Tashar talabijin Channels ta ce cikin kayan da aka arce aka bari da hango rundunar ‘yan sandan sun hada da mota Volkswagen Golf da lambar LUY 899 KV.

Mutum daya ya fada hannu

Haka ‘yan sanda suka yi ta binsu har zuwa wajen wani sha-tale-tale, aka cafke wani direba mai suna Dahiru Muazu, yanzu haka yana hannu ana bincike.

Ta hannun wannan mutumi ne jami'an 'yan sandan su ke kokarin cafko sauran wadanda ake zargi da fashin da suka sulale da aka nemi a cin masu.

An sace Sarki a Kogi

A wani kauye da yake cikin karamar hukumar Kabba Bunu a jihar Kogi, an ji labarin an yi garkuwa da wasu Bayin Allah uku a cikin daren shekaran jiya.

‘Yan bindiga sun yi nasarar sace Mai martaba Sarkin Oghara da wasu manya da ake ji da su a kasar. A wajen harin ne kuma aka rasa wata ma'aikaciyar fada.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan daba sun kashe dan sanda, sun jikkata wasu jami'ai da yawa a wata jiha

Asali: Legit.ng

Online view pixel