Bernard Arnault, mutumin da ya Nemi Hambarar da Elon Musk a Matsayin Attajirin Duniya

Bernard Arnault, mutumin da ya Nemi Hambarar da Elon Musk a Matsayin Attajirin Duniya

  • A ‘yan watannin baya, akwai mutane biyu da suka sha gaban Bernard Arnault a jerin Attajiran Duniya
  • Sai da Bernard Arnault ya sha gaban duk wani Mai kudi a Disamban nan, ya mallaki Dala Biliyan $185
  • Bafaranshen mai shekara 73 da haihuwa ne ya mallaki kamfanonin Louis Vuitton, Berluti da TAG Heuer

US - A sakamakon rasa Dala biliyan 44 da Elon Musk ya yi a ranar Larabar nan, mujallar Forbes ta nuna Bernard Arnault ya dare kujerar attajirin Duniya.

Daga baya Bernard Arnault wanda shi ne shugaban kamfanin Louis Vuitton da ya mallaki Dala biliyan 185.3 ya sauka daga wannan matsayi ba da dadewa ba.

Jama’a za su so jin wanene Arnault wanda ya yi abin da babu wani mahaluki da ya taba yi, ya sha gaba Musk a wajen arziki tun watan Satumban shekarar 2021.

Kara karanta wannan

Jonathan Ya Bude Baki Ya Yi Magana Kan Takara a APC da Sake Neman Mulki

A duk Duniya, babu wani kamfanin kayan kwalliya da suka sha gaban na Louis Vuitton. Dattijon ya cin ma nasara ne bayan shekaru fiye da 40 yana wahala.

Wanene Bernard Arnault?

Mun dauko bayanin tarihin ‘dan kasuwar daga shafin Rahoton Business Insider.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haihuwa da karatun boko

An haifi Arnault a watan Maris na shekarar 1949, ya yi karatu a fannin Injiniyanci a wata babbar makarantar koyon aiki watau Polytechnic a kasar Faransa.

Bayan gama karatu a 1971 ya fara aiki a kamfanin mahaifinsa, har ya zama shugaba a 1978.

Bernard Arnault
Bernard Arnault Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Kamfanin LVMH Moët Hennessy

Daga baya Arnault ya saye Ferret-Savinel, ya canzawa kamfanin suna domin a samu riba da kyau. Sannu a hankali sai ya fi kowa hannun jeri a Louis Vuitton.

A shekarar 1989 ya zama shugaban LVMH Moët Hennessy bayan sayen hanunn jarin $2.6bn

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Elon Musk Ya Rasa Matsayinsa Na Attajirin Duniya, Kudinsa Ya Ragu Da N1.6tn Cikin Awanni

Yau kamfanin LVMH Moët Hennessy watau - Louis Vuitton yana hannun Bernard Arnault. Duka ‘ya ‘yansa na aiki da rassan kamfanin: Berluti da TAG Heuer.

Aure da ‘Ya ‘yansa

Attajirin ya auri Anne Dewavrin a 1973, suka haifi ‘ya ‘ya biyu. Bayan shekaru kusan 17 suka rabu, Arnault ya auri Bakanadiya, Hélène Mercier a shekarar 1991.

Dewavrin ta haifawa Arnault Antoine da Delphine Arnault. Matar da ya sake aure ce ta haifi Alexandre, Frédéric, da Jean. Dukkansu suna aiki a kamfanin shi.

Antoine ce ake ganin za ta gaji mahaifinta a Louis Voiton idan ya mutu. Babbar ‘diyar ta fara aiki ne a McKinsey & Co, yanzu ita ce mataimkiyar shugaba a LV.

Facaka da kudi

Attajirin yana yawo ne a jirgin samansa,ya kuma saba kashe kudi wajen shakatawa. Sai da ya kashe $96.4m a kan gidaje kurum a yankin da yake zama a Amurka.

Sabon tsarin CBN

Kara karanta wannan

Nagode Mama: Aminu Adamu ya Bada Hakuri a Fili, Yayi Alkwari Zai Gyara Halinsa

A makon nan aka samu labarin wata sanarwa cewa Babban bankin Najeriya watau CBN ya fitar da wasu dokokin cire kudi a duka bankunan Kasar nan.

Daga watan Disamban nan, adadin kudin da mutum zai iya cirewa ta banki ko na’urar POS ko kuma ATM ya ragu zuwa N100, 000 a kowane mako.

Asali: Legit.ng

Online view pixel