Sababbin Sauye-Sauye 9 da Gwamnan Bankin CBN Ya Kawo Wajen Cire Kudi

Sababbin Sauye-Sauye 9 da Gwamnan Bankin CBN Ya Kawo Wajen Cire Kudi

  • A yanzu kudin da mutum zai iya cirewa ta na’urar ATM a tsawon mako daya bai isa ya wuce N100,000 ba
  • Haka zalika masu amfani da na'urar POS za su iya cire N20,000 ne kacal a kowace rana, N100, 000 a duk mako
  • Bankuna za su daina dura takardun kudin da suka haura N200 a ATM, hakan zai hana tsabar kudi yawo sosai

Abuja - Babban bankin Najeriya na CBN ya kawo sababbin tsare-tsare ga masu cire kudi. Hakan na zuwa ne yayin da za a fito da sababbin Nairori.

Legit.ng Hausa ta bi sanarwar da CBN ya bada, ta tattaro dokoki da tsare-tsaren da aka kawo.

Matakan da aka fitar sun kunshi:

1. Kudin da mutum zai cire

Daga yanzu yawan kudin da mutum zai iya dauka daga banki a cikin mako guda shi ne N100, 000. Kamfanoni kuma za su iya cire abin da bai wuce N500, 000.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: CBN ta Fitar Da Sabbin Matakai 5 Kan Hada-Hadar Kudi a Bankuna

2. La’ada a kan fiye da adadin

Duk wanda zai fitar da abin da ya wuce wannan kaidi da aka yi, sai ya biya 5% na abin da zai cire. Misali, mai kokarin cire N200, 000 sai ya ba banki N10,000.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

3. Kamfanoni za su biya 10%

Idan har kamfani yana son cire duk abin da ya zarce N500, 000 a cikin mako ko N100, 000 a rana, sai ya biya banki 10%, misali N100, 000 a kan duk N1m kenan.

4. Amfani da Cheque

Sabon dokar ta haramtawa mutum zuwa banki ya karbi N50, 000 ta takardar Cheque da aka rubuta masa. Ba a canza sauran dokoki amfani da Cheque a banki ba.

Naira
Shugaban Kasa da Jami'an CBN Hoto: www.arise.tv
Asali: UGC

5. Kudin da ke cikin ATM

Idan mutum ya je na’urar ATM domin ya cire kudi daga asusunsa, ba zai samu takardun kudin N500 ko N1000 ba, abin da zai samu ‘yan N200 ne zuwa kasa.

Kara karanta wannan

Ban Taba Sa Rai Ba: Fasto Idahosa Ya Bada Labarin Yadda Kwankwaso Ya Ba Shi Takara

6. N100, 000 a duk mako ta POS

Kamar yadda abin yake a bankuna, mai amfani da na’urar POS ba zai iya zarar sama da N10, 000 a cikin mako ba, an bada damar a cire N20, 000 ne a kullum.

7. Idan an shiga matsin lamba fa?

Akwai yiwuwar a samu kai a cikin hali na matsi da dole a bukaci kudi masu yawa, a nan za a bada dama ga mutum ko kamfani ya iya cire N5m da N10m.

8. Takardun shaida

Ana bukatar katin zama ‘dan kasa, fasfo, lasisin tuki da BVN da sa hannun wani babban jami’i kafin a ba mutum damar cire abin da ya kai N5m a banki.

9. Sai an samu amincewar banki

BBC tace dole ne shugaban bankin da ake mu’amala da shi ya rubuta takardar amincewa ga duk mai neman cire abin da wuce kudin da aka kayyade

Najeriya za tayi asara

Kara karanta wannan

2023: Malamin addini ya fadi ta yadda shugaban Najeriya na gaba ya kamata ya fito

A maimakon duk rana a hako ganguna miliyan biyu, an rahoto Babagana Monguno yana cewa ganga miliyan daya ake samu a halin yanzu a Najeriya.

Janar Babagana Monguno mai ritaya ya nuna muddin ba a dauki matakin da ya dace ba, N10tr ba za su shiga baitul-mali kamar yadda aka yi lissafi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel