Wani Matashi da ba a San da Zaman Shi ba, Yace Gwamnan Najeriya ne Mahaifinsa

Wani Matashi da ba a San da Zaman Shi ba, Yace Gwamnan Najeriya ne Mahaifinsa

  • An samu wani ‘Dan shekara 27 da ya je kotu, yana cewa Gwamna Babajide Sanwo-Olu shi ne Mahaifinsa
  • John Aikpokpo-Martins shi ne Lauyan da ya tsayawa Emmanuel Sanwo-Olu, yana karar Gwamnan Legas
  • Wannan mutumi yana zargin Gwamnan ya samu alaka da mahaifiyarsa a garin Delta a shekarun 1994/95

Delta - Ana shari’ar nasaba a wata babban kotun jiha mai zama a Effurun a karamar hukumar Uvwie da ke jihar Delta da Gwamna Babajide Sanwo-Olu.

Jaridar Tribune tace wani Emmanuel Sanwo-Olu mai shekara 27 yana ikirarin Gwamnan jihar Legas na mahaifinsa, ya kuma ce ya tabbata da haka.

Emmanuel Sanwo-Olu yake cewa mahaifiyarsa ta sanar da shi cewa Mai girma Babajide Sanwo-Olu ne mahaifinsa, daga baya ta auri wani mutumin.

“Ni dai ina so in ga mahaifina ne, shekaru 27 da suka wuce, ban ga mahaifi na ba.”

- Emmanuel Sanwo-Olu

Mahaifi yana daula, yaro yana aikatau

A halin yanzu wannan mutumi mai ‘ya ‘ya uku yace yana yi wa mutane aiki ne domin ciyar da iyalinsa, yayin da mahaifinsa ke gidan gwamnati.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

John Aikpokpo-Martins Esq wanda shi ne Lauyan da ya tsayawa Emmanuel Sanwo-Olu wajen shigar da kara a kotu, yace an fara sauraron shari’arsu.

Gwamnan Najeriya
Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo Olu Hoto: businessday.ng
Asali: UGC

Ba a shari'a da Gwamnoni

Daily Trust ta rahoto John Aikpokpo-Martins yana cewa Lauyoyin Gwamnan Legas sun bukaci ayi watsi da karar domin doka ta ba gwamnoni kariya.

A cewar Lauyan, ya roki kotu ta ba su dama a kira Gwamna Sanwo-Olu domin ayi masa gwajin DNA, yace ta haka za a san gaskiyar ikirarin da suke yi.

Rahoton ya nuna shi ma Aikpokpo-Martins bai shiryawa shari’ar ba, ya bukaci Alkali ya ba su lokaci domin su zauna da bangaren wadanda ake tuhuma.

Maganar da ake yi an daga shari’ar mail amba EHC/148/2022 sai zuwa ranar 17 ga Junairun 2023. A nan za a san mataki na gaba da kotu za ta dauka.

Ana zargin Gwamnan mai-ci ya samu alaka da mahaifiyar mai karar, Grace Moses a 1994.

Za a kara FMC a Katsina

Ana kukan babu asibitocin tarayya a Kano, Kaduna, Sokoto, Borno, Akwa-Ibom, Edo, Anambra, Ebonyi da Enugu, sai ga rahoto za a sake gina wani a Katsina.

A kasafin karshe na Mai girma Muhammadu Buhari, gwamnatin tarayya za ta kashe N500m domin samar da katafaren asibitin na biyu a jihar shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel