An gano Ameerah da tayi ikirarin ‘Yan bindiga sun shiga Abuja, sun yi garkuwa da su 17

An gano Ameerah da tayi ikirarin ‘Yan bindiga sun shiga Abuja, sun yi garkuwa da su 17

  • A ranar Talatar da ta gabata, Ameerah Sufiyan ta fito shafin Twitter tana cewa an yi garkuwa da su a Abuja
  • Bayan kwanaki uku, ‘Yan Sanda sun gano Ameerah Sufiyan, amma babu tabbacin dauke ta aka yi a gida
  • Yayin da ‘Yan Sanda ke bincike, an fara samun labari da alama wannan Baiwar Allah kitsa labarin ta yi

Abuja - Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya sun yi nasarar gano Ameerah Sufiyanu, wata Baiwar Allah da tayi ikirarin an yi garkuwa da ita a ranar Talata.

A ranar 14 ga watan Yuni 2022, Ameerah Sufiyanu ta shaidawa Duniya cewa wasu ‘yan bindiga sun yi ram da ita, tare da wasu mutane 17 a birnin Abuja.

Tun lokacin aka shiga neman inda aka kai ta domin kuwa ta iya bayyana inda ta ke da halin da su ke ciki. Budurwar tayi wannan ne ta shafinta na Twitter.

Kara karanta wannan

An ceto matar jigon APC da aka yi garkuwa da ita a Minna a tashar motar Kano da ke Maiduguri

Kwanaki uku da aukuwar lamarin, dakarun ‘yan sanda sun bada sanarwa da ta bayyana cewa an gano Ameerah, amma akwai alamar tambaya game da ita.

Anya kuwa? - 'Yan Sanda

Kamar yadda sanarwar ‘yan sandan ta tabbatar, babu tabbacin cewa an yi garkuwa da wannan yarinya tare da wasu mutane 17, yadda ta rayawa al’umma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bugu da kari, ‘yan sanda sun ce su na binciken gaskiyar duk abin da ya wakana zuwa yanzu.

Ameerah Sufiyan
Hoton Ameerah Sufiyan da NPF Hoto: @Ameerah_sufyan
Asali: Twitter

A karshen sanarwar da ta fito a yau Juma’a, 17 ga watan Yuni 2022 da kimanin karfe 2:00 na rana, jami’an tsaro sun ce za su yi cikakken bayanin bincikensu.

Meya faru da Ameerah?

Tun farko, Jafar Jafar wanda fitaccen ‘dan jarida ne, ya nuna akwai abin duba a wannan labarin.

Da yake bayani a Twitter, Jafar ya ce a ranar da abin zai faru, Ameerah ta bar gida ne salin-alin kamar yadda wani da ke aiki kusa da gidansu ya bada labari.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: ‘Yan bindiga sun sace wani dan jarida a jihar Kudancin Najeriya

Wannan yarinya ta bar gidan ne bayan ta ci abincin safe, sai ta fadawa mahaifiyarta cewa ana buga masu gida. Daga nan sai ta fice ba tare da wani ya ankara ba.

Abin mamaki shi ne gidansu yana kusa da ofishin ‘yan sanda da ke unguwar Apo a Abuja. A lokacin, Budurwar ta iya aika sakonnin sauti ga wasu abokanta.

A karshe Ameerah wanda wata kawarta tace ba ta da lafiya, tayi ikirarin wadannan ‘yan bindiga sun kai ta wani asibiti ne da ke garin Legas domin ta wartsake.

Matsalar tsaro a Najeriya

A farkon makon nan aka samu rahoto cewa Tokunbo Ajasin ya jagoranci zanga-zangar da mutane suka shirya a garin Ibadan saboda matsalar tsaro da ake fama da ita.

Wannan matashi yana cikin ‘ya ‘yan tsohon gwamnan jihar Ondo, Marigayi PA Adekunle Ajasin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel