Muje Zuwa: Wata Mata Ta Hango Alheri Bayan da Dangote Ya Samu Kishiya Wajen Gina Matatar Mai

Muje Zuwa: Wata Mata Ta Hango Alheri Bayan da Dangote Ya Samu Kishiya Wajen Gina Matatar Mai

  • Wata ‘yar Najeriya ta bayyana ra’ayinta game da kyakkyawar fafatawa tsakanin Abdul Samad Rabiu mai kamfanin BUA da Aliko Dangote
  • Ta yi nuni da cewa, mai kamfanin BUA ya kuma yi koyi da Dangote wajen gina matatar mai na kansa kamar yadda ya yi a siminti, sukara, da garin filawa
  • Ta yarda cewa zazzafar hamayyar da ke tsakanin attajiran biyu na Najeriya za ta amfanar ‘yan kasa kana ta habaka tattalin arziki

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

Najeriya - Wata mata ‘yar Najeriya ta bayyana matsayarta da kuma ra’ayinta game da fafatawa da hamayya tsakanin Dangote da AbdulSamad, wanda ya fara gina matatar mai a Legas.

A wani rubutun da ta yada a Twitter, ta lura cewa, BUA ya bi sahun Dangote wajen fara aikin gina matatar mai a Awka ta jihar Akwa Ibom.

Kara karanta wannan

Fitaccen malamin addini ya yi hasashen makomar Najeriya ana tsaka da wahala

Ta kuma gamsu cewa, matsanancin gasa da hamayyar da ke tsakanin attajiran biyu zai taimakawa kasar tabbas, musamman wajen habaka tattalin arziki.

Dangote ya samu kishiya a fannin man fetur
BUA zai fara matatar mai, Dangote ya samu kishiya | Hoto: @gveiv/Twitter
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakazalika, ta yi hasashen cewa, hakan zai zama mai amfani ga ‘yan Najeriya a gaba ta fuskoki da dama.

Abinda matar ke cewa

Ta rubuta a shafinta na Twitter cewa:

“Tofa. BUA/ mai kamfanin Abdul Rabiu yanzu ya bi sahun Dangote/ Aliko Dangote sau da kafa...a kusan duk abin da yake yi.
“A yanzu BUA na gina matatar mai mai girman pd 200,000 a jihar Akwa Ibom...don samar da kayayyakin man fetur ga Najeriya da Afrika. Na fahimci BUA zai fara gadan-gadan a cikin 2024. Ina son wannan gasa...saboda kasuwanci.”

Dalilin da yasa har yanzu simintin BUA ke da tsada

A wani labarin, biyo bayan sanar da rage farashin simintin BUA zuwa N3,500 a watan Oktoba, gar yanzu farashinsa bai sauya daga yadda yake a kasuwanni kafin sanarwar ba.

Kara karanta wannan

Wike vs Fubara: Jerin sunayen manyan yan siyasa 4 da tsohon gwamnan Ribas ya raba gari da su

Idan baku manta ba, rahotonmu na baya ya naqalto yadda kamfanin ya sanar da ragin tare da fadin dalilinsa na yin haka.

Simintin mai nauyin 50kg ana siyar dashi a farashin da ke tsakanin N5,500 ko sama a yankuna daban-daban na Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel