Zargin matan asibiti da fasikanci: Budaddiyar wasika zuwa ga Dr. Abdallah Gadon-Kaya

Zargin matan asibiti da fasikanci: Budaddiyar wasika zuwa ga Dr. Abdallah Gadon-Kaya

  • An ji Dr. Abdallah Usman Gadon Ƙaya ya na zargin malaman asibiti da laifin yin lalata da junansu
  • Shehin malamin ya bayyana wannan ne a wani bidiyonsa da yake yawo a kafafen sada zumunta
  • A cewar Abdallah Usman Gadon Ƙaya, mata da ke aikin dare su kan yi fasikanci a dakunan asibiti
  • Wani marubuci, Ibrahim El-Caleel ya rubutawa Shehin wasika ta musamman a kan wannan batun

Ibrahim El-Caleel ya rubuta wannan doguwar wasika, ba jaridar Legit.ng Hausa ba.

Legit.ng Hausa ta samu wasikar da Malam Ibrahim El-Caleel ya rubutawa Abdallah Usman Gadon Ƙaya da ya jefi ma’aikatan jinya da mummunar alfasha.

A wannan budaddiyar takarda da Ibrahim El-Caleel ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ja hankalin babban malamin addini, Abdallah Gadon Ƙaya.

El-Caleel ya yi masa nasiha da ya kiyaye abin da yake fada a matsayinsa na wanda ake sauraron maganarsa, tare da jan-kunnensa kan daukar jita-jita.

Kara karanta wannan

An shiga jimami: Jama'a sun zub da hawaye yayin da amarya ta rasu ana gab da aurenta

A cewarsa, irin wadannan kalamai za su jawo mutane su kara kauracewa matan da ke aikin asibiti, a lokacin da suke shan wahalar samun mazajen aure.

Baya ga haka, kalaman za su zuga mata su guji shiga aikin jinya, alhali ana bukatarsu a asibitoci.

A wannan wasika, za a ji matashin malamin ya yi kira ga Sheikh Gadon-Kaya ya rika bincike kafin ya rika yada duk labarin da mutane su ka kawo masa.

Har ila yau, El-Caleel ya bada shawara ga wannan malami ya maida hankali wajen fadakar da al’umma a kan kawo gyara, ba kokarin yin akasin hakan ba.

A karshe marubucin ya nemi Malamin ya tsaya a kan karatun addinin da yake yi, ya daina shagala da wasu labarai da yake samu daga wajen mutane.

Kara karanta wannan

Majalisar Dattawa za ta dauki mataki kan kudin karatun jami'a domin talaka ya samu ilmi

Sheikh Gadon-Kaya
Sheikh Abdallah Usman Gadon-Kaya da asibiti Hoto: www.istockphoto.com/Rilwan Diso
Asali: UGC

Buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga Dr Abdallah Usman Gadon Ƙaya (حفظه الله)

1. Akaramakallah, Assalamu alaikum. Fatan Malam yana cikin ƙoshin lafiya da albarkar rayuwa. Allah Ya saka da alheri bisa hidimar karantar da addini da ake yi kullun, amin.
2. Maƙasudin rubuta wannan wasiƙar shine don ankarar da Malam akan bidiyoyin shi da suke yawo inda yake yawan bada labarai iri-iri. Waɗannan báƙin labarai suna da ban mamakin ji, musamman kasancewar suna fitowa ne daga majlisin ilimi ko mimbarin Jumu'ah.
3. Tashar AfricaTV3 a shafin su na Facebook sun saki wani faifai na Malam, inda kake hakaito wani labari da kace wani ne ya baka shi, akan yadda ma'aikatan lafiya mata da maza suke mu'amalar banza tsakanin su a aikin dare, wato "night shift".
4. Akramakallah, Allah ne Ya taimaki wannan al'ummar tamu. Mutane sun amince sosai da malamai saboda amana ta ilimi. Hatta ƴan siyasa sun gane ƙimar malamai a idanun mutane, don haka suke raɓar malamai don su sahhale su mutane su zaɓe su. Duk wannan yana nuna irin darajar malamai ne a idanun jama'a.

Kara karanta wannan

Akwai matsala: Miyagu sun sace $4bn daga arzikin Najeriya a 2021, su na sayen makamai

5. Duk mutumin da mutane suka amince mishi, to wani babban nauyi ne ya hau kanshi. Mutumin ya zama jagorar al'umma, ya zama abin koyi. Maganganun sa suna da matuƙar tasiri cikin al'umma. Ashe kenan dole irin wannan mutumi ya riƙa auna maganganun shi kafin ya furta su. Duk labarin da zai bada, to ya tabbatar da ingancin sa. Ko da labarin ƙarya ne aka bashi, in fa ya bada shi, to mutane da yawa zasu karɓi wannan labarin a matsayin gaskiya ne.

Labari mai hadari

6. Labarin da Malam yace an bashi gameda fasiƙancin ma'aikatan lafiya cikin dare, labari ne da cikin sauƙi zai iya rusa al'ummar mu. Musulman Arewa an bar mu a baya a fannin boko. Don haka a shekarun baya muke fama da ƙarancin ma'aikata, ƙo'ina bamu da mutane. Hatta asibitoci. Komai ustazanci ko sheɗancin mutum, idan shi ko matar sa bata da lafiya, wani zabgegen ƙato ne, ma'abocin shirka zai duba shi ko matar shi. Malamai da jagororin mu suka nuna kuskuren mu, aka zaburar da mutane suka shiga boko sosai. Cikin ikon Allah yanzu mun fara samun sauƙi kaɗan. Ana samun mata musulmai sosai cikin ma'aikata lafiya. Don haka yanzu asirin matan mu ya fara rufuwa. Idan sun je asibiti da lalura, suna iya cin sa'a ƴan uwan su mata su duba su. Ka ga mutuncin matan mu ya rufu.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Likitan Bello Turji da ke masa jinya da kawo masa kwaya ya shiga hannu

7. Malam, a halin yanzu fa su kansu ma'aiktan lafiya mata suna cikin ƙalubale. Mazaje na gudun auren su saboda ganin basu da wadataccen lokacin kula da yara da gida. Yanzu kuma da Malam yake hakaito labarin fasiƙanci da ake da sunan kwanan asibiti, to kamar fa Malam yana ƙara sanyawa ne a kyamaci auren ma'aikatan lafiya. Don haka duk Uba mai hankali, ba zai yarda ɗiyar sa ta karanta Medicine ko Nursing ba. Don kada ta gama ta kasa samun miji, kuma sannan a gari a riƙa mata kallon ƴar iska. Shima mijin ma'aikaciyar asibiti, yanzu an jefa mishi shakku ya riƙa zargin matarsa da cin amanar aure.
8. Wannan shine illar bada irin waɗannan labarai daga mimbarai na masallatan Jumu'ah, ko daga majalis na ilimi. Kuma saboda Allah, Akarakallah, shin kayi binciken wannan labarin da aka baka? Yanzu da fake news yayi yawa, don me mutum zai karɓi labari koma wani iri ne, sannan ya zo yayi gini akai, har yana sharhi?

Kara karanta wannan

Kisan gillan Hanifa: Ministan ilimi ya yabawa kokarin da gwamnatin Kano ke yi

9. Mu ƙaddara ma labarin nan tabbas gaskiya ne. A matsayin Malam, shin wannan hanyar da ya bi itace hanyar da za'a gyara mafsadar? Ai fasiƙi da fasiƙa ana samun su a ko'ina, ba sai cikin ma'aikata ba. Mata nawa ne suke zaune a gida basa aiki, amma kuma suke fasiƙanci a bayan idanun mazajen su? Shin hatta a nan Kano labarai nawa ne aka bada gameda matan aure mazauna gida waɗanda suke maɗigo a bayan idanun mazajen su? Don haka lamarin fa bashi da wani alaƙa da aikin asibiti, ko sharar titi ko zaman gida. Fasiƙi da fasiƙa duk inda suke basa fasa fasiƙancin su.
10. Ashe kenan hikima shine a cigaba da faɗakarwa game da zina, da zunubin cin amanar aure. Sannan a ja hankalin mata da maza da suke aiki da juna cewa su kiyaye haddin shari'ah. Su kiyaye amanar mazajen su da tarbiyyar iyayen su. A cigaba da waɗannan nasihohi akan kowa. Wannan shine zai taimaki al'ummah. Ba wai a jefawa mutane zargin wasu ƴan uwa da fasiƙanci ba.

Kara karanta wannan

Uwargida ta dannawa mijinta dutsen guga har lahira don ya dirkawa wata ciki

11. Ina so Malam ya sani cewa ma'aikatan lafiya ma basa son aikin kwanan nan! Babu wacce zata yi naƙuda ta haifo yara sannan da daddare ta fi son zuwa "kwana da ƙarti" fiye da kwana da ƴaƴan ta. Basa so. Abin ya zama dole ne. Saboda mutane suna kamuwa da cuta cikin dare su buƙaci kulawa ta gaggawa; mata sukan shiga naƙuda da daddare. To idan yanzu babu musulmai mata irin mu a asibitocin, me aka yi kenan? Ai an koma gidan jiya kenan! Cikin daren Alaramma Ustaz Abu Fulan zai ɗauko matar sa Malama Ummu Fulan ya damƙa ta hannun Dr Samuel ya duba ta! Shi kuma wannan wani irin sharri kenan? Daga nan kuma wani irin labari Malam yake tunanin za'a fara kawo mishi daga asibitoci?
12. Sannan, na ga Malam yayi bidiyo yana gyara kalamansa cikin wancan labari. Wannan yayi kyau, duk da dai wasu sun ce Dr Abdalla yayi wannan ne saboda ƙungiyar ma'aikatan lafiya sun yi barazanar maka shi a kotu saboda yayi ƙoƙarin ɓata musu suna. Wannan dai shine matsalar da ake gudu. Irin wannan abin shine yake jawowa malamai raini. A ƴan shekarun nan Malam yayi ta fama da irin waɗannan matsaloli. Sai yayi magana, daga baya kuma sai ya janye ko yayi ƙoƙarin abinda bature ke cewa "damage control". Akaramakallah, wannan abin anya ba zai taɓa girmar ka a idanun jama'a ba kuwa?

Kara karanta wannan

Yadda yunkurin zawarcin Jonathan, a ba shi takara a APC ya sha ruwa tun kafin a kai 2023

Malam ya tsaya a karatunsa

13. Da ace Malam zai tsaya iyakar gundarin ilimin da yake karantarwa, to da mun ce Alhamdulillahi. In ma labarin ne, Malam sai ya taƙaitu ga iya abinda shi da kanshi ya sheda. Saboda an hakaito wa Malam labarai da yawa waɗanda ƙarshe dai labaran nan suka jefa Malam cikin rikici. Ashe lokaci bai yi ba da Malam zai hana mutane kawo mishi labarai?
14a. Ina mai rufe wannan nasiha tawa da Hadisin Manzon Allah ﷺ da yake cewa, (كفى بالمرء كذبا أن يحدث بكل ما سمع).
14b. Al-Imam Abdurrahman bnul Jawziy (Rh) da yazo bayanin hadisin nan, sai yace:
‎(فيه تأويلان، أحدها: أن يروي ما يعلمه كذبًا، ولا يبينه فهو أحد الكاذبين، والثاني: أنَّ يكون المعنى بحسب المرء أن يكذب؛ لأنَّه ليس كلُّ مسموع يصدق به، فينبغي تحديث الناس بما تحتمله عقولهم)
16. Allah Ya ƙarawa Malam lafiya da albarka. Allah Ya taimake mu akan harsunan mu. Allah Ya kiyaye mana mutuncin mu.

Kara karanta wannan

Hanifa: Sanusi II, mayan malamai sun yi kalamai masu zafi a kan wanda ya yi kisan gilla

Wassalatu wassalamu ala RasulilLah.
Naka a musulinci,
Ibrahiym

Martanin da mutane su ke yi a Facebook

Kawo yanzu dai kalaman malamin su na ta jawo surutu, har kungiyar ma’aikatan jinya su na barazanar maka shi a kotu saboda zargin ya na bata masu suna.

Abdul Halim Ringim wanda malamin asibiti ne a garin Zariya, ya yi wa Gadon-Kaya raddi, ya ce abin da malamin musuluncin yake fada ya yi nesa da gaskiya.

A shafinsa na Facebook, Ringim ya bayyana cewa ana ware dakunan mata da na maza a asibiti, sannan kuma ba barci kowa yake yi idan ana aikin daren ba.

Wannan shi ne maganar da Dr. Abdullahi Dahiru ya yi a Facebook a yammacin ranar Lahadin nan.

“Idan mutum ya ce akwai asibitin da ake cakuda maza da mata maaikata suna aikin kwana sai a tambaye shi wane asibiti ne?
Ma'aikatan jinya fa in su na aikin kwana, ba fa barci suke ba. Su na da wajen aikinsu a tsakiyar dakin marasa lafiya.

Kara karanta wannan

Shekaru 24 da faruwar lamari, Janar Abdussalam ya fadi yadda Abiola ya mutu a daure

Ba na jin dai za'a iya kawo misalin wannan asibitin da maza ma’aikata suke tarayya da mata a daki bare shugabannin asibitin su gyara.

- Dr. Abdullahi Dahiru

Amma irinsu Rilwan Adam Diso su na ganin malamin ya yi gaskiya, akwai bukatar ayi gyara a aikin asibiti, ya ce mutane ne suke sha'awar sukar Dr. Gadon-Kaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel