Akwai matsala: Miyagu sun sace $4bn daga arzikin Najeriya a 2021, su na sayen makamai

Akwai matsala: Miyagu sun sace $4bn daga arzikin Najeriya a 2021, su na sayen makamai

  • Shugaban bankin UBA Group, Mista Tony Elumelu ya ce Najeriya tayi asarar $4bn a shekarar bara
  • Wadannan kudi sama da Naira tiriliyan 1.6 sun tafi wajen barayin da ke satar danyen man kasar
  • Tony Elumelu ya ja hankalin al’umma a kan yadda makudan kudi suke shiga hannun miyagun mutane

Abuja - Tsakanin watan Junairu zuwa Satumban 2021, Najeriya tayi asarar kusan Dala biliyan hudu a dalilin satar danyen mai a yankin Neja-Delta.

Shugaban kamfanin Heirs Holding da bankin nan na UBA Group, Tony Elumelu ya bayyana wannan. Daily Trust ta fitar da wannan rahoto a jiya.

Asarar da aka tafka a yankin na Neja-Delta kurum ya kai Naira tiriliyan 1.68 a kudin Najeriya.

Mista Tony Elumelu ya yi wannan jawabi da yake gabatar da wata takarda a wata lacca ta musamman da ya shirya a makarantar sojojin Najeriya.

Kara karanta wannan

2023: Jerin abubuwa 6 da za su tare hanyar Atiku Abubakar ya zama Shugaban Najeriya

Strategic leadership: My business experience

Rahoton ya ke cewa Elumelu ya gabatar da laccarsa kan abubuwan da ya gani wajen aiki, an yi wa laccar taken ‘Strategic leadership: My business experience.’

Attajirin ya ce satar danyen man da ake yi ya zama barazana ga zaman lafiyan Najeriya, ganin yadda miyagun mutane suke da tulin dukiya a hannunsu.

Tony Elumelu
Tony Elumelu tare da Shugaban kasa Hoto: theeagleonline.com.ng
Asali: UGC
“Mai da gas su na fuskantar barazana daga sata. Satar mai a yankin Neja-Delta ya zama abin da yake ci wa kasa tuwo a kwarya.”
Za mu hako danyen mai, sai barayi su sace kusan ganguna 50, 000 duk rana. A wurina wannan ya na bukatar a kira taron kasa.”
“A ra’ayi na, wannan ya na cikin hadari mafi muna da muke fuskanta a matsayinmu na kasa, saboda akwai dukiya a hannun bata-gari.”

Kara karanta wannan

Dare daya: Yadda dan crypto ya zama miloniya a wata sabuwar duniyar crypto wai ita NFT

“Mutanen da ba su biyan kudin haraji, kuma mutanen da ba ka da iko da su. Wannan kasar ba kalau ta ke ba.” - Tony Elumelu.”

Ana sayen makamai

Vanguard ta rahoto Elumelu yana mai cewa tsakanin Junairu da Satumban 2021, Najeriya tayi asarar $4bn a hannun miyagun mutanen da ke sayen makamai.

‘Dan kasuwan ya ce mutane su maida hankali wajen zaben shugabanni nagari da za su iya shawo kan matsalar, kuma ya yi kira na musamman ga jami’an tsaro.

Takaita haihuwa a Najeriya

Gwamnati ta fara kokarin kayyade yawan iyali, an shigo da tsarin rage al'umma. A halin yanzu an ji cewa duk shekaru ana samun karin mutum miliyan shida.

Muhammadu Buhari ya bukaci a dauki matakan gaggawa kan yawan haihuwa da ake yi ta hanyar fadada shirin samar da hanyoyin bada tazarar haihuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel