Alheri danko ne: Bidiyon mai tallan pure water yana raba wa fursunoni kudi ya ja hankalin jama'a

Alheri danko ne: Bidiyon mai tallan pure water yana raba wa fursunoni kudi ya ja hankalin jama'a

  • Wani mai talla ya bi wasu fursunoni a cikin motar hukumar gyaran hali a Ajah ta jihar Legas inda ya basu mamaki
  • Rahotanni sun ce an ga bidiyon mai tallan ruwan gora yana ba da 70% cikin 100% na kudin da ya tara ga fursunonin
  • Da ruwan da yake sayarwa a kansa, matashin dan Najeriya ya bi su ta taga yana raba musu kudin

Legas - ‘Yan Najeriya sun yi wa wani dan talla fatan alheri bayan da bidiyonsa da yake nuna kirkinsa ga fursunonin da ke cikin motar gidan gyaran hali ya yi ta yawo a shafukan sada zumunta.

A cikin wani faifan bidiyon da aka yada a shafin Instagram, dan Najeriyan da ke sana’ar tallan ruwan sha ya tunkari wata motar gidan gyaran hali da ke dauke da fursunoni.

Kara karanta wannan

Ci da ceto: Duk da yaye rufin gidansa domin ya biya kudin fansa, wasu na kokarin damfarar dattijo

Mai tallan ruwa ya ba da mamaki
Alheri danko ne: Bidiyon mai tallan pure water yana raba wa fursunoni kudi ya ja hankalin jama'a | Hoto: @instablog9ja
Asali: Instagram

Da kayansa na ruwan kwalba a kansa, dan tallan ya mika wa fursunoni makudan kudade ta taga.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a yayin da ake cinkoson ababen hawa a unguwar Ajah da ke Legas.

An ce wanda ya dauki faifan bidiyon ya karbi wayar dan tallan ne domin daukar bayanan asusunsa amma ya dauki bidiyon lamarin saboda ya narke ya burge shi.

Kalli bidiyon:

Jama'a a kafar sada zumunta sun mayar da martani

@adekola_omobolanle ya ce:

"Wow ina addu'a ya daukaka, kuma Allah ya taimaka ma kaddararsa ta same shi da wuri wannan shine ma'anar idan yana da hali zai zama mai kyautatawa a rayuwa kuma yana son taimakon wadanda ke kasa da dashi."

@kiddokinging ya ce:

"Yi kyauta ba tare da ihu ba albarka ce a gare shi da tsararrakinsa ba irin wasu mutane a nan ba da ke son duniya ta san suna kyauta."

Kara karanta wannan

Cin amana: Ango ya kama amaryarsa da kwarto bayan kwana 9 da aurensu

@princewilson_ ya ce:

"Kuma bai yi hakan ba don kyamara ko dan a gani ba wannan kirkir ne na gaske. Allah ya albarkace ka kuma ya ninka maka sau 1000 mutumi na."

@adrenalynjunky ya ce:

"Misali balo-balo da ke nuna ba wai sai ka mallaki duniya ne za ka yi alheri ba. Wasu mutane suna jin sai ka kai wani mataki kafin ka yi irin wannan, kullum suna kan roko saboda basu basa tausayin wasu. Ina fatan aikinsa na alheri ya koya muku cewa ba haka bane, Allah ya saka masa da alheri."

@officialbobbyfredrick__ ya ce:

"Idan zai iya yin wannan lokacin da ba shi da komai, shin ba zai yi da yawa ba lokacin da yake da karin abin da zai bayar?... Allah ya albarkaci wadannan mutane masu irin wannan zuciyar kuma su zama tsafatattu masu haske kullum."

A wani labarin, Kaosarah Abisola Oyesiji ita ce dalibar da ta yi fice a jami’ar nan ta Al-Hikmah, Ilorin, jihar Kwara a shekarar nan, ta kammala karatu da maki 4.59.

Kara karanta wannan

Gwamnatina ba za ta yi watsi da ku ba: Shugaba Buhari ya yi jajen kisan 'yan Zamfara

Jaridar Daily Trust ta rahoto Kaosarah Abisola Oyesiji tana bayanin irin sadaukar da rayuwarta ta da tayi domin ganin ta samu gagarumar nasara a jarrabawarta.

A kaf sashen koyon ilmin akanta, Kaosarah Abisola Oyesiji ce ta zama gwarzo a shekarar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel