Tagwayen Asali: Shahararrun tagwaye sun angwance da wasu tagwaye a Kano

Tagwayen Asali: Shahararrun tagwaye sun angwance da wasu tagwaye a Kano

  • Wasu tagwaye sun yi aure, inda suka auri wasu tagywaye masu kama daya a jihar Kano cikin makon nan
  • Rahoto ya bayyana yadda angwayen suka bayyana yadda suka jima suna addu'ar Allah ya basu mata tagwaye
  • Sun ce Allah ya amsa addu'arsu, kuma anyi aure yayin da shahararrun 'yan wasan kwaikwayo a Arewa suka halarta

Kano - Rahoton Daily Trust ya ce, shahararrun tagwayen Kano da ake yi wa lakabi a duniyar Hausa hip-pop da suna ‘Tagwayen Asali’ sun yi aure a cikin wani gagarumin salo tare da wasu tagwayen Katsina, Hassana da Hussaina a Kano.

Haka dai tagwayen da suka yi aure da ’yan tagwaye masu kama da juna suka burge masoyansu da auren inda hakan ya dauki hankulan masana’antar nishadantarwa ta Arewa.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Mummunar gobara ta yi kaca-kaca da wani gida, uwa da jaririnta sun kone a Kano

Tagwaye sun angwance
Tagwayen Asali: Shahararrun tagwaye sun angwance da wasu tagwaye a jihar Kano | Hoto: newsday.com.ng
Asali: UGC

An san su da tsarin sutura da salon waka a tare, tagwayen sun ba masoyansu mamaki saboda sun kasance tare a a harkar nishadantarwa na tsawon shekaru tare da aiki a ma'aikatar gwamnatin tarayya daya.

A cewar angwayen, sun dade suna addu’a da azumi domin su samu ‘yan mata tagwaye da za su aura, inda suka kara da cewa Allah ya karbi addu’arsu ya ba su tagwaye masu kama daya da za su aura daga Katsina.

Shafin LindaIkeji'sBlog ya rahoto tagwayen angwayen na cewa:

"Auren tagwaye masu kama daya shine buri daya da muke dashi a rayuwarmu kuma da yardar Allah mun samu."

A lamari mai ban sha'awa, bikin ya samu halartar tagwaye da dama wadanda abokan angwaye da amare ne.

Hakazalika shahararren Mawakin Hausa Hamisu Breaker ya nishadantar da baki yayin bikin auren.

Kara karanta wannan

Yadda jami'an DSS 5 suka taimaka min na yi garkuwa da kwastoma na, Wanda ake Zargi

Ango ya kama amaryarsa da kwarto bayan kwana 9 da aurensu

A wani labarin, wani ango ya bayyana aniyarsa na kawo karshen auren da ke tsakaninsa da matarsa kan zargin da ya shiga tsakani.

Labarin da aka yada ya nuna cewa mutumin ya kama matarsa tana sheke ayarta da wani kato kwanaki kadan bayan aurensu.

A cewar labarin da @chuddyOzil ya wallafa a shafinsa na Twitter, mutumin da matarsa sun yi aure ne a ranar 27 ga watan Disamba, 2021. Sai dai rikicin ya soma ne lokacin da mutumin ya kama matarsa da wani mutum a wurin da suke shakatawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel