Innalillahi: Mummunar gobara ta yi kaca-kaca da wani gida, uwa da jaririnta sun kone a Kano

Innalillahi: Mummunar gobara ta yi kaca-kaca da wani gida, uwa da jaririnta sun kone a Kano

  • Wata mummunar gobara ta yi kaca-kaca da wani gida a jihar Kano, lamarin da ya kai ga mutuwar wasu mutane
  • Rahoto ya bayyana cewa, wata mata mai suna Zainab da dan ta mai shekara daya sun rasu yayin wannan gobara
  • Kakakin rundunar kashe gobara ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana yadda rundunar ta ba da gudunmawar kashe wutar

Kano - Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da rasuwar wani yaro mai suna Sulaiman Usaini dan shekara daya da mahaifiyarsa mai suna Zainab Yusha’u mai shekaru 25 a hanyar Gwarzo da ke Gidan Kaji a jihar Kano.

Alhaji Saminu Abdullahi, jami’in hulda da jama’a na hukumar ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Kano, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan sanda sun shiga tsakani yayin da kwarto ya kashe mijin daduronsa

Yadda gobara ta yi barna a jihar Kano
Innalillahi: Gobara ta yi sanadiyyar mutuwar uwa da jaririnta a jihar Kano | Hoto: dailynigerian.com
Asali: Twitter

Abdullahi ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da safiyar Asabar 8 ga watan Janairun 2022.

A cewarsa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Mun sami kiran waya da misalin karfe 07:00 na safe. daga wani mutum Usman Nura kuma nan take muka aika da tawagarmu zuwa wurin da abin ya faru da misalin karfe 07:08 na safe.”

Da yake bayyana inda gobarar ta auku, Abdullahi ya ce gini ne na bene mai tsayi kusan kafa 35 da 20, daki daya ya dan kone yayin da gobarar ta kone falon gidan gaba daya.

Ya ce an mika gawarwakin wadanda abin ya shafa ga mijin marigayiya Zainab, wato Malam Usaini.

Ya kara da cewa:

"Da kyakkyawan kokari na jami'an kashe gobara, mun sami damar shawo kan gobarar domin kada ta bazu zuwa gidan makwabta."

Hakazalika, kakakin rundunar ya shawarci jama’a da su bi ka’idojin tsaro domin gujewa abubuwan da ba a zata ba.

Kara karanta wannan

Yadda Gobara ta kama kasuwar Nguru dake jihar Yobe ranar Asabar

Gobara ta yi kaca-kaca da katafaren kamfani a jihar Kano

Gobara ta kone wani katafaren kamfanin kera ababen katako da ke Kano mai suna Alibert Furniture.

Daily Nigerian ta tattaro cewa gobarar ta tashi ne da sanyin safiyar yau Litinin, inda ta kone kamfanin da ke kan hanyar Murtala Mohammed a cikin babban birnin kasar.

An tattaro cewa jami’an tsaro biyu na kamfanin sun samu raunuka daban-daban kuma an garzaya da su asibiti.

Duk da cewa har yanzu ba a gano musabbabin tashin gobarar ba, shaidu sun alakanta gobarar da matsalar wutar lantarki da ta samu daga taransifomar kamfanin.

Jami’an kwana-kwana sun yi nasarar kashe gobarar amma har yanzu wasu sassa na ginin na ci gaba da cin wuta har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

A wani labarin, an samu hargitsi a ranar Laraba, 3 ga watan Nuwamba, yayin da wata gagarumar gobara ta cinye wasu gine-gine da shaguna a Owode Onirin, daura da unguwar Ikorodu Road a Legas.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun sace wani shugaban kwastam mai ritaya a gonarsa a Kwara

Vanguard ta rahoto cewa a lokacin da jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Legas, suka isa wurin da lamarin ya faru, wasu fusatattun matasa sun far musu.

An ce matasan sun kai wa jami’an hari ne saboda rahotanni sun ce sun isa wurin a makare bayan an yi ta kiran su yayin da wutar ta kama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.