Kamar wasa: Yadda wani mutum ya ci gasar N413,410,000 amma aka bashi wani zabi

Kamar wasa: Yadda wani mutum ya ci gasar N413,410,000 amma aka bashi wani zabi

  • Wani mahaifi a Amurka ya samu nasarar canza rayuwarsa bayan fita sayen madara da cakulat ga yaransa a watan Disamba 2021
  • Akan hanyarsa ne ya yanke shawarar gwada sa'arsa a wata caca, kuma abin ya kayatar sosai har ya ci kyautar $1m (N413,410,000)
  • A karshe Dennis ya zabi a rage yawan kudin a bashi maimakon karbar cikakken adadin na tsawon shekaru 30

Wani mahaifi, Dennis Willoughby, ya gamu da babban abin mamakin rayuwarsa bayan ya fita zuwa masana'antar 7-Eleven domin sayen cakulatt ga 'ya'yansa.

A hanyarsa ta zuwa can, Dennis ya yanke shawarar sayen tikitin caca daga Virginia Lottery mai suna Jackpot Platinum $1,000,000 kuma ya yi nasara a cacar, in ji CNN.

Wanda ya ci gasar biliyoyi, Dennis Willoughby
Kamar wasa: Yadda wani mutum ya ci gasar biliyoyi daga fita sayen cakulat din yara | Hoto: CNN
Asali: UGC

Ya so a bashi kudi kadan

A tarihi, shi ne mutum na biyu da ya taba lashe babbar kyautar caca kuma har yanzu akwai sauran mutum guda da ake sa ran zai lashe kyautar, in ji WYOMING News.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wajen gabatar da kyautar, an baiwa mutumin zabin ko dai ya karbi duka $1m (N413,410,0000) inda za ake bashi wani kaso duk shekara a tsawon shekaru 30 ko kuma ya karbi dala 640,205 (N264,667,149.05), ban da kudin haraji.

Mutumin ya zabi zabi na biyu. Dennis yanzu yana da fiye da kudin sayen kowane nau'in cakulat da yake so ga yaransa.

Garin dadi: Bidiyon 'yan sanda na raba wa masu mota kudi maimakon karba daga hannunsu

Jami'ai daga Sashen 'yan sanda na Ocala da ke Florida a Amurka, an gansu a cikin wani faifan bidiyo da ke rera taken Santa Claus.

A wani faifan bidiyo da Ayo Ojeniyi ya yada, wani jami’in dan sanda ya tare wata mata mai mota inda ya ce zai ba ta kudi $100 (N41,016). Da matar ta ji haka, sai ta tambaye shi ko da gaske ne zai yi hakan?

Bayan ya ba ta kudin, matar da ta kasa gaskata abin da ya faru a baya ta zabga kururuwa:

"Na gode, Yesu!"

Asali: Legit.ng

Online view pixel