'Yan Najeriya sun cika sa ido, tsohon minista ya siffanta halin 'yan Najeriya

'Yan Najeriya sun cika sa ido, tsohon minista ya siffanta halin 'yan Najeriya

  • Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, yace ‘yan Najeriya da dama sun saka masa ido kan duk wani abu da yake yi, kama daga abinci har sutura
  • Kayode dan jam’iyyar APC ya ce ya yi mamakin al’amarin da ya bayyana a matsayin nuna damuwa
  • FFK kamar yadda ya bayyana ya ce ya kasance kanun labarai kwanan nan game da dangantakarsa da tsohuwar matarsa da kuma rikicinsa da EFCC

Femi Fani-Kayode, tsohon ministan sufurin jiragen sama kuma jigo a jam'iyyar APC mai mulki, ya ce 'yan Najeriya da dama sun damu da lamurranshi.

A wani sako da ya wallafa a Facebook a ranar Laraba, 29 ga watan Disamba, ministan ya ce yana matukar mamakin yadda ‘yan Najeriya ke nuna damuwa akansa.

Tsohon ministan harkokin jiragen sama, Femi Fani-Kayode ya magantu kan yadda ake sa masa ido
'Yan Najeriya sun cika sa ido, tsohon minista ya bayyana halin 'yan Najeriya | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: Twitter

Ya rubuta:

“Damuwar da ‘yan Najeriya ke nunawa kan FFK yana ba ni mamaki.

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda wasu suka ba hammata iska a yayin da ake tsaka da wa’azi a coci

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Abin da yake yi, abin da yake fada, inda ya tafi, abin da yake sawa, wanda yake tare da shi, abin da yake ci, abin da yake sha, abin da yake rubutawa, abin da yake tunani, abin da yake so, abin da ba ya so,, wanda yake gani da dai sauransu.!
"Nuna damuwa ne da kuma kaunarsa!"

Legit.ng ta rahoto cewa a baya-bayan nan Fani-Kayode ya shiga kanun labarai kan gayyatar da hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta yi masa da kuma alakarsa da tsohuwar matarsa Precious Chikwendu.

Bamu taba kwanciyar aure dashi ba, amma 'ya'yanmu hudu, inji tsohuwar matar Fani-Kayode

A wani labarin, jaruma Precious Chikwendu ta roki kotu da ta ba ta cikakkiyar damar kula da ‘ya’yanta da ta haifa tare da Femi Fani-Kayode.

Kara karanta wannan

Ba zata sabu ba: Iyayen amarya sun fasa aurar da 'yarsu bayan ganin gidan da ango zai aje ta

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa tsohuwar sarauniyar kyau din ta ce ta haifi ’ya’yanta ne ta hanyar yi mata dashen 'ya'ya a kimiyyance yayin da aka tilasta mat zaman aure dashi.

Chikwendu ta bayyana cewa bata taba kasancewa a zaman aure da Fani-Kayode ba saboda bai biya kudin aurenta ba.

Tsohuwar sarauniyar kyawun ta bayyana cewa aurenta da Fani-Kayode yana cike da bala'i, tashin hankali a cikin gida, wulakanci a idan duniya, da rashin kusantar juna saboda rashin iya tabuka komai a jima'i da dai sauran matsaloli.

Asali: Legit.ng

Online view pixel