Bidiyon yadda wasu suka ba hammata iska a yayin da ake tsaka da wa’azi a coci

Bidiyon yadda wasu suka ba hammata iska a yayin da ake tsaka da wa’azi a coci

  • Wani abun al'ajabi ya afku a cocin Olivet Baptist da ke Chattanooga, Tennessee a ranar Lahadi, 26 ga watan Disamaba, 2021 tsakanin mambobin cocin
  • An dai ba hammata iska ne tsakanin wasu mambobin cocin su biyu a yayin da fasto ke tsaka da yin wa'azi
  • Rigima ya fara ne lokacin da wani mamba ya tawo ya daurawa wani da ke zaune yana sauraron wa'azi naushi, nan take shima ya mayar masa inda suka dambatu

An sha yar dirama a cocin Olivet Baptist da ke Chattanooga, Tennessee a ranar Lahadi, 26 ga watan Disamaba, 2021, lokacin da mambobin cocin biyu suka ba hammata iska yayin da faston ke wa’azi.

An gano wani dan cocin a bidiyo yana tunkarar wani da ke zaune hankali kwance yana sauraron sakon da faston ke isarwa.

Kara karanta wannan

Ba zata sabu ba: Iyayen amarya sun fasa aurar da 'yarsu bayan ganin gidan da ango zai aje ta

Kawai sai mutumin da ba a bayyana kowanene ba ya kaiwa na zaunen naushi, lamarin da yasa shima ya tashi ya far masa inda suka bai wa hammata iska.

Bidiyon wasu mutane 2 da suka ba hammata iska a yayin da ake tsaka da wa’azi a coci
Bidiyon wasu mutane 2 da suka ba hammata iska a yayin da ake tsaka da wa’azi a coci Hoto: Fasanmi Paul Abiola
Asali: Facebook

Faston, Bishop Kevin Adam ya yi kokarin hana mabiyan nasa fada amma sai suka ci gaba inda aka jiyo shi yana cewa “Ka daina, Marcus. Marcus, daina mana.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai kuma da yake magana bayan fadan, faston ya bayyana cewa mutumin da ke sanye da farar riga fitowarsa kenan daga cibiyar gyara hali kuma kai tsaye ya tunkari matashin faston da ke zaune a kujerar gaba.

Ya ci gaba da bayyana cewa ya yiwu mutumin ya gigice ne saboda bai san a ina yake ba.

Malamin ya bayyana cewa bayan sun yi nasarar tausarsa, ya fashe da kuka inda ya kara da cewa mutumin zai koma cibiyar gyara hali, kuma cocin ta bashi cikakken goyon baya.

Kara karanta wannan

Bakon lamari: Bidiyon dan sanda na raba wa matafiya buhunan shinkafa ya jawo cece-kuce

Kalli bidiyon wanda wani mai amfani da shafin Facebook Fasanmi Paul Abiola ya wallafa:

Bai zo a littafi mai tsarki ba: Kirista ta caccaki masu bikin Kirsimeti

A gefe guda, wani bidiyo da shafin @instablog9ja ya wallafa a Instagram ya nuno lokacin da wata mai wa'azi ta baje kolinta na yin wa'azi a wajen na'urar ATM bayan wani ya taya ta murnar Kirsimeti.

Da take bayani kan addininta, matar ta bayyana cewa babu wani waje a littafi mai tsarki (Injila) da aka yi bikin Kirsimeti, inda ta bayyana hakan a matsayin kafirci.

Ta ci gaba da bayyana cewa bikin ya bai wa mutane da dama kafar yin duk wasu abubuwan shaidanci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel