Sabbin zafafan hotunan Shatu Garko, sarauniyar kyau ta Najeriya da suka girgiza Instagram

Sabbin zafafan hotunan Shatu Garko, sarauniyar kyau ta Najeriya da suka girgiza Instagram

  • Shatu Garko ta zama mace ta farko da ta lashe gasar sarauniyar kyau sanye da Hijabi a duniya yayin da ta lashe gasar Miss Nigeria 2021
  • Jarumar 'yar jihar Kano ta kasance cikin ‘yan takara a gasar shekara-shekara ta kyau karo na 44 da aka gudanar a ranar Juma’a 17 ga watan Disamba
  • Kwatsam sai kafafen sada zumunta suka cika da labaru da hotunan wannan matashiya da ta lashe wannan gasar kyau a Najeriya

A ranar Juma’a 17 ga watan Disamba ne aka kafa tarihi a Landmark Centre da ke Victoria Island, Legas cikin dare mai cike da kyakykyawan yanayi yayin da aka samu wacce ta karbi kambu na farko a gasar kyau sanye da Hijabi a duniya.

Shatu Garko, ‘yar shekara 18 ta zama sarauniyar kyau na Miss Nigeria ta 44, inda ta gaji Etsanyi Tukura, ‘yar asalin jihar Taraba, a gasar karo na 43 na Miss Nigeria 2019.

Kara karanta wannan

Makudan miliyoyi da abubuwa 4 da ya kamata ku sani game da sarauniyar kyau ta Najeriya, Shatu Garko

Aishatu Garko, sarauniyar kyau
Wasu zafafan hotunan Shatu Garko, sarauniyar kyau ta Najeriya masu ban sha'awa | Hoto: Shatu Garko
Asali: Instagram

Wadanda suka zo bayan ta na daya da na biyu su ne Nicole Ikot da Kasarachi Okoro.

A cikin wannan rahoton, Legit.ng ta tattaro wasu kyawawan hotuna guda biyar na sarauniyar kyau mai Hijabi, kamar yadda ake gani a shafinta na Instagram..

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

1. Kyawawar Bahaushiya

A wannan hoton, an ga sarauniyar kyan sanye da kayan al'adun Hausawa wanda ke wakiltar al'ummar Hausawa daga yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

A cikin wannan hoton an gan ta a cikin riga da zane na atamfa da wata alkyabba mai kyalli da dauke ido.

Kalli hoton:

2. Shiga a yanayi na kawa

Kamar sauran mata masu sanya hijabi da yawa a duniya, Garko ba ta fito kafafen sada zumunta don tallata kyawunta da sunan kwalliya ba.

A cikin wannan hoton, an gan ta tsaye cikin wata doguwar riga dinkin atamfar maxi mai launin toka-toka tare da kallabi akanta ga kuma jaka a rataye.

Kara karanta wannan

Waiwaye a 2021: Haziƙan Ɗaliban Najeriya 4 Da Suka Karya Tarihin Da Ba a Taɓa Zaton Wani Zai Iya Ba

Duba kasa:

3. Sauyin salo

A wannan karon, sarauniyar kyau ta canza shiga zuwa shigar zamani amma dai kan ta a rufe, gashinta daure cikin salo da kallabi mai launin dorawa.

Garko ta girgiza kafafen sada zumunta yayin da ta sanya wani wando da bakar riga 'yar ciki inda kuma ta sanya farar riga a sama.

Ganewa idonku:

4. Kyawawan tufa masu furanni

A cikin wani yanayi mai kyau, sabuwar sarauniyar ta sanya wata riga mai zanenfure sannan ta nannade gashin kanta a salon rawani gwanin burgewa. Zane-zane mai launin shudi a kusa da kafadun rigar ya karawa kayan kyau.

Duba hoton a kasa:

5. Shigar Denim Slay

Wannan hoto da ta dauka a wani fili yana fitar da wani bangare na daban na kyau ga sarauniyar kyau Shatu Garko.

Anan an gan ta sanye da wando na siriri kuma matsattsaye mai dauke da saman chiffon da launin shudi, ta fito babu takalmi zaune a kan ciyawa a wani fili.

Kara karanta wannan

Alkali ya fallasa lauyan da yayi yunkurin ba shi cin hanci a Plateau

Kalli hoton:

Sabuwar sarauniya ta lashe kyautar kudi har N10m, zama na shekara 1 a wani katafaren gida, sabuwar mota, da sauran damarmakin tallata manyan hajoji.

A cewar masu shirya gasar, bikin na nuna kyawawan halaye na matan Najeriya a duk shekara.

Makudan miliyoyi da abubuwa 4 da ya kamata ku sani game da sarauniyar kyau ta Najeriya, Shatu Garko

A baya kunji cewa, a ranar Asabar ne labari ya karade kafafen watsa labaran Najeriya kan sanar da wata 'yar jihar Kano, Shatu Garko a matsayin sarauniyar kyau ta Najeriya.

Shatu Garko ‘yar shekaru 18 da haifuwa da ake kallo da Hijabi ta ciri tuta a gasar kyau ta Miss Nigeria karo na 44 wannan shekara ta 2021.

An nada ta a matsayin sarauniya ta 44 ne a gasar a lokacin tantacewar karshe na gasar da aka gudanar a Legas a daren Juma’a, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Fadar Shugaban kasa ta jero tulin nasarorin Shugaba Buhari yayin da ya cika shekara 79

Asali: Legit.ng

Online view pixel