Matashi ya ci A1 8 a jarrabawarsa ta WAEC, yana neman taimako zai karanta likitanci

Matashi ya ci A1 8 a jarrabawarsa ta WAEC, yana neman taimako zai karanta likitanci

  • Wani matashi dan Najeriya mai suna Praise Ojonugwa Abba yana neman a taimaka masa domin ci ga da karatunsa har zuwa jami'a bayan ya samu sakamako mai kyau a WAEC
  • Praise wanda a halin yanzu yake neman taimakon ’yan Najeriya masu hali ya bayyana cewa yana son karatun likitanci a matakin karatun jami'a
  • Matashin dan Najeriya ya fito ne daga jihar Kaduna kuma yanzu ya shiga sahun daliban da suka nuna cancantar su

Kaduna - Wani matashi dan Najeriya mai suna Praise Ojonugwa Abba ya nunawa duniya cewa akwai hazikai a kasar nan domin ya samu makin A1 a kusan dukkan darussan da ya rubuta a WAEC, face harshen Ingilishi inda ya samu B3.

Praise wanda ya fito daga jihar Kaduna ya kammala karatunsa na sakandare a Faith Academy da ke Kaduna.

Kara karanta wannan

Na yi farin ciki da aka kama ni, na san laifi na ke yi, in ji mai kaiwa 'yan bindiga bayanan sirri a Zamfara

A wani sako da aka aika wa Legit.ng an ce yaron na bukatar ya karanci likitanci a ciki ko wajen kasar nan.

Dalibi Praise Ojonugwa Abba
Dan Najeriya ya ci A1 9 a jarrabawar WAEC, yana neman taimako zai karanta likitanci
Asali: Original

Yana bukatar ayi masa goma na arziki

Matashin ya ba da lambar wayarsa ga masu son taimaka masa kamar haka; 09077643439.

Wasu daga cikin darrusan da ya samu makin A1 a cikinsu sun hada da Mathematics, Biology, Chemistry, da Physics.

Wani bangare na kiran tallafin da aka turo ya karanta:

“Don Allah idan wannan ne kadai alherin da za ku iya yi wa dan Adam, don Allah ku yi wa wannan yaro. Babu wanda ya san shi amma za ku iya taimakawa wajen daga shi ga duniya. Na san har yanzu muna da mutane masu kirki da tausayi a kasar nan da za su taimaka masa ya cimma burinsa. Yana bukatar tallafi domin ya karanci likitanci a Najeriya ko a wajen kasar. Za mu iya taimaka masa wajen cimma wannan buri sannan ya hidimtawa bil'adama a kasarmu."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: EFCC ta sanya gwamnan Anambra a jerin sunayen wadanda take nema

Ba wannan ba ne karo na farko a Najeriya

Wannan dai ba shi ne karon farko da wani dan Najeriya da zai fito da kyakkyawan sakamako a jarabawar WAEC ba.

Kwanakin baya, wata budurwa mai suna Chiemela Stephanie Madu ta samu makin A1 a dukkan darrusan da ta rubuta a jarabawar WAEC ta kuma baiwa mutane da dama mamaki.

Dalibar da ta fito daga jihar Imo ta samu maki 345 a jarrabawar shiga jami'a ta UTME a Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Owerri.

Stephanie, duk da haka, ta ce tana da mafarkin karatun likitanci a kasar Kanada. ‘Yan Najeriya da dama sun yaba da hazakar matashiyar dabibar.

Dan baiwa: Yadda yaro dan shekara 2 ya koyi yaren jafananci cikin sa'o'i 24

A waye kuwa, wani yaro dan kasar Ghana mai shekaru biyu, Isaiah Gyamfi, ya koyi yadda ake rubutu da kirge cikin Turanci, Sifaniyanci, Faransanci da warware matsalolin ninkawa da debewa a lissafi.

Kara karanta wannan

Minista Pantami ya jero dalilai 5 da suke nuna Najeriya a shirye take a bangare kasuwanci

Ya kuma koyi kirge har zuwa 40 a cikin yaren Jafananci cikin kasa da sa'o'i 24, kamar yadda kafar labarai a kasar Ghana, Yen ta ruwaio.

Mahaifiyarsa mai shekaru 30, Jazelle, daga Kudu maso Yammacin London, ta shaida wa jaridar Mirror cewa yaron yakan iya fahimtar sabbin bayanai cikin sauki tun yana dan shekara biyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel