Latest
Fubara ya dawo daga hutun makonni biyu, bayan ya gana da Tinubu a Landan. An ce gwamnan da aka dakatar ya kuma gana da Wike, ya durkusa har gwiwa yana neman gafara.
Wasu tsagerun 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hare-haren ta'addanci a jihar Sokoto. 'Yan bindigan sun hallaka mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.
Rahotanni da muke samu sun tabbatar da cewa ƴan bindiga da ake zargin yaran Bello Turji ne sun kai farmaki garuruwa da ke karamar hukumar Isa a Sokoto.
Wani dan Amurka da ya shafe shekaru 18 yana shan gubar maciji da ya sha cizon maciji sama da sau 200 ya ce ya sadaukar da aikin don rigakafin cizon maciji.
Fitaccen mawakin nan, Dauda Kahutu wanda aka fi sani da Rarara ya sako sabuwar waƙar da ya yi wa Tinubu a wurin liyafar da aka shiryawa shugaban ƙasa.
Shugaban Bola Tinubu ya bukaci gwamnonin Najeriya da su maida hankali kan sauke nauyin da ke kansu. Ya bukaci su yi watsi da masu kokarin karkatar musu da hankali.
Kamfanin Meta da ya mallaki Facebook, Instagram da Whatsapp ya yi barazanar rufe Facebook da Instagram saboda harajin Dala miliyan 290 da aka daura masa.
Rahotanni sun tabbatar da cewa rundunar ‘yan sanda ta mamaye gidan Galadiman Kano da ke Galadanci a karamar hukumar Gwale, bayan naɗin muƙamin har biyu a jihar.
Gwamnan jihar Ogun ya bayyana cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu zai kaddamar da kamfanin sarrafa auduga mafi girma a jihar Ogun. Mutane 250,000 za su samu aiki.
Masu zafi
Samu kari