Latest
Surukin Rabiu Kwankwaso, Mukhtar Zakari ya ce bai yi karyar takardun karatu ba kamar yadda aka yi masa hukunci, yanzu ya daukaka kara domin rike kujerarsa.
Wani binciken jami’an tsaro na DSS ya gano ana neman a kai hari a jirgin kasan Abuja-Kaduna. ‘Yan bindiga ba su hakura ba, su na son kai hari na biyu daga 2022.
Bola Tinubu ya dauki aro a wajen tsohon shugaban kasar, bai bada babbar kujerar Ministan fetur ba. A lokacin Muhammadu Buhari, shi ne babban Minista na mai.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai rantsar da sabbin ministocinsa a ranar Litinin, 21 ga watan Agusta, a cibiyar taro na fadar shugaban kasa, Abuja da 10:00am.
Tsohon sanatan Kaduna, Shehu Sani ya soki zabar tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle da Shugaban Kasa Bola Tinubu ya yi a matsayin ministan tsaro.
Tsagerun yan bindiga sun harbe Misis Peace Chinyereugo, matar faston cocin Vineyard of Grace Dominion Assembly, Rev. Samuel Chinyereugo, a Benin, jihar Edo.
Kamfanin NNPC ya karbi bashin Dala biliyan uku a bankin AFRIEXIM da ke kasar Masar don kawo daidaito a farashin Naira da kuma kasuwannin canjin kudade a kasar.
Sanata Barau Jibrin, ya roki yan Najeriya musamman mambobin jam'iyyar APC, da su taya jam'iyyar da addu'a don ta yi nasara a kotun zaben gwamnan jihar Kano.
Ƴan bindiga sun kai wani sabon farmaki a jihar Ebonyi da ke yankin Kudu maso Gabashin Najeriya inda suka sace wasu ma'aurata tare da diyar su da direban su.
Masu zafi
Samu kari