Sababbin Ma'aikatu Da Tinubu Ya Kirkiro Wajen Nada Ministoci a Gwamnatin Tarayya

Sababbin Ma'aikatu Da Tinubu Ya Kirkiro Wajen Nada Ministoci a Gwamnatin Tarayya

  • Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu zai rantsar da ministocin gwamnatinsa a ranar Litinin mai zuwa
  • Sakataren gwamnatin tarayya ya fitar da sanarwa game da yadda shugaban kasa ya raba masu aiki a ofis
  • A wani sabon salo a Najeriya, Hannatu Musawa za ta Ministar fasaha, al’adu da tattalin arzikin fikira

Abuja - Legit.ng Hausa ta bi jerin ministocin da ma’aikatar da aka ba kowanensu, ta lura da wasu ‘yan canje-canje da aka samu a gwamnati.

Akwai ma’aikatun tarayyar da aka yi wa garambawul, aka kara masu aikin da za su yi.

Bayan nan kuma akwai ma’aikatun da wannan ne kusan karon farko da aka kirkire su a tarihin Najeriya, a kan su za a fara nada ministocinsu.

Ministoci a Gwamnatin Tarayya
Bola Tinubu ya zabi Ministoci Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Ma'aikatun da aka yi wa kwaskwarima

1. Ministan kula da muhalli

Kara karanta wannan

Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Karin Haske Kan Lokacin Da Tinubu Zai Rantsar Da Ministocinsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A baya sai dai kurum a kira wannan minista da mai kula da muhalli, a wannan sabon salo da aka fito da shi, an kara masu da sunan kula da muhallin.

2. Ministan harkar ruwa

Baya ga harkar ruwa da madatsan da aka san ma’aikatar da ita, Farfesa Joseph Utsev da mataimakinsa za su hada da aikin tsabta a Najeriya.

3. Ministan noma

Za a rantsar da Sanata Abubakar Kyari ne a matsayin ministan noma da na harkar samar da abinci, wannan canji ya karfafa aikin dadaddiyar ma’aikatar.

4. Ministan lafiya

Farfesa Ali Pate da Tunji Alausa za su shiga ofis a matsayin ministoci masu jagorantar harkar kiwon lafiya da kuma kula da walwalar jama’an kasa.

5. Ministan labarai

Aikin da ke gaban Mohammed Idris Malagi ya fi karfin yada labarai kurum, zai hada da wayar da kan al’umma a kan manufofin gwamnati da cigaban kasa.

Kara karanta wannan

Ana Sukar Sanatoci, Ma’aikatan CBN Sun Cinye Naira Biliyan 260 a Alawus a Shekara 2

6. Ministan tattalin arzikin zamani

Mun fahimci baya ga harkar sadarwa da musamman tattalin arzikin zamani, nauyin da za a daurawa Bosun Tijjani zai hada da kirkire-kirkire a bangaren.

7. Ministan tattalin arzikin teku

Wani ofishi da Bunmi Tunji-Ojo zai rike shi ne Ministan tattalin arzikin teku da ruwa. Tsohon 'dan majalisar na jihar Ondo zai jagoranci kula da rayuwar ruwa.

8. Ministan tattalin arzikin al’adu

Kamar yadda aka yi tunani, a bangaren tattalin arzikin, akwai Hannatu Musawa da za ta jagoranci sabuwar ma’aikatar da za a bar wa dawainiyar al’adu da fikira.

9. Ministan yawon bude ido

Gwamnatin Bola Tinubu za ta dawo da ma’aikatar da aka manta da ita – yawon bude ido. Lola Ade John zai yi kokarin ganin ana samun kudi daga shakatawa.

10. Ministan gas

Gas ya samu ma’aikata mai zaman kan shi a Najeriya. Zuwa yanzu ba a san wa zai zama mai gidan Ekperikpe Ekpo wanda mu ka yi hasashe game da mukaminta.

Kara karanta wannan

Kyau Ya Hadu Da Kyau: Diyar Biloniya Indimi Ta Amarce Da Babban Dan Kasuwar Kasar Turkiyya

11. Ministan makamashi

A makon gobe Adebayo Adelabu zai zama ministan makamashi na kasa. Jama’a sun yi tunanin Nasir El-Rufai zai rike wannan sabubuwar ma’akatar tarayyar.

12. Ministar jin kai

Da alama babu ruwan Betta Edu da walwalar al’umma da tallafin gaggawa idan ta shiga ofis, sai dai a yanzu aikin ma’aikatarta ya hada da yaki da talauci.

13. Ministan kasafin kudi

Bola Tinubu ya ware kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki daga ma'aikatar kudi. Atiku Bagudu wanda masanin tattalin arziki ne zai rike wannan kujera.

14. Ministan gidaje

A maimakon yadda aka hada ayyuka, gidaje da lantarki tare a 2015, gwamnati mai-ci ta nada Ahmad Dangiwa ya zama babban ministan harkar gidaje.

Babu Ministan man fetur

Kun ji labari cewa Mai girma shugaban Najeriya Bola Tinubu ya dauki aro a wajen tsohon shugaban kasar, bai bada babbar kujerar Ministan fetur ba.

A lokacin Muhammadu Buhari, shi ne babban Ministan harkokin man fetur na kasa daga 2015-2023, a lokacin mulkin soja, Buhari ya rike wannan kujera.

Asali: Legit.ng

Online view pixel