'Yan Bindiga Sun Sace Ma'aurata Da Diyarsu a Jihar Ebonyi

'Yan Bindiga Sun Sace Ma'aurata Da Diyarsu a Jihar Ebonyi

  • Wani magidanci mai suna Ajah Chibuzo tare da matarsa da diyar su sun faɗa hannun miyagun ƴan bindiga
  • Ƴan bindigan dai sun yi awon gaba da mutanen ne suna kan hanyar su dawowa gida a ƙaramar hukumar Ivo ta jihar Ebonyi
  • Hukumomi sun bayyana cewa an tura da jami'an tsaro domin.ceto mutanen tare da cafke miyagun da suka sace su

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Ebonyi - Ƴan bindiga sun yi awon gaba da wani magidanci mai suna Ajah Chibuzo tare da matarsa, ɗiyar su mai shekara 12 da direban su a jihar Ebonyi.

Ƴan bindigan sun sace ma'auratan ne da ɗiyar su da direban a Mil 2 Ishiagu, akan titin hanyar Okigwe-Ishiagu cikin karamar hukumar Ivo ta jihar, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Daga Karshe An Bayyana Dalilin Da Ya Sanya Jirgin Sojin Saman Najeriya Ya Yi Hatsari a Jihar Neja

Yan bindiga sun sace ma'aurata a jihar Ebonyi
'Yan bindiga sun yi awon gaba da wasu ma'aurata a jihar Ebonyi Hoto: Theguardian.com
Asali: UGC

Ma'auratan suna kan hanyar dawowa ne zuwa gida a ranar Talata da yamma a cikin wata mota ƙirar Sienna, mai ɗauke da lambar KWL 941 PD lokacin da ƴan bindigan suka tattara suka tafi da su cikin daji.

An tattaro cewa, daga bayan an ɗauko motar daga inda aka sace su inda aka kai ta ofishin ƴan sanda na Ishiagu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An tabbatar da aukuwar lamarin

Har yanzu ƴan sanda ba su tabbatar da aukuwar lamarin ba, amma hadimin gwamnan jihar Ebonyi kan harkokin tsaro a ƙaramar hukumar Ivo, Hon. Ike Cletus ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Cletus wanda ya nuna damuwarsa kan yadda garkuwa da mutane ke yawan ƙaruwa a yankin, ya ɗora alhakin hakan akan rashin jajircewar da ƴan sakai su ke a yankin.

Da yake magana da manema labarai a birnin Abakaliki, shugaban ƙaramar hukumar Ivo, Emmanuel Ajah, ya bayyana cewa an aike da tawagar jami''an tsaro domin bin sahun ƴan bindigan.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Badda Kama Sun Yi Awon Gaba Da Bayin Allah Masu Yawa a Jihar Arewa

"Yanzu haka jami'an tsaro sun yi wa dajin ƙawanya domin tabbatar da ceto mutanen da aka sace da cafke ƴan bindigan da ake zargi." A cewarsa.

'Yan Sanda Sun Fatattaki 'Yan Ta'adda a Katsina

A wani labarin kuma, ƴan ta'adda sun kwashi kashin su a hannun jami'an ƴan sanda a jihar Katsina.

Jami'an ƴan sanda sun samu nasarar halaka ɗan ta'adda ɗaya da makamai a wata fafatawa da suka yi da miyagun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel