An Kama Matashi Bisa Laifin Satar Karafa Masu Tsada a Makabartar Legas

An Kama Matashi Bisa Laifin Satar Karafa Masu Tsada a Makabartar Legas

  • Dubun wani matashi mai shekaru 28 ta cika, yayin da aka gurfanar da shi gaban kuliya bisa laifin sata a maƙabarta
  • Matashin ya bude ƙaburbura inda ya sace ƙarafan da aka rufe mamacin da ke kwance a ciki da su
  • An bayyana cewa darajar ƙarahunan da ake zargin matashin ya sata sun kai naira miliyan ɗaya da dubu ɗari

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Ikeja, Legas - Wata kotun Majistare da ke zamanta a Ikeja jihar Legas, ta aike da wani matashi ɗan shekara 28 zuwan gidan yari a ranar Larabar da ta gabata.

Ana zargin matashin da satar ƙarafan da ake rufe mamata da su a wata maƙabarta da ke Legas, da kuɗinsu ya kai naira miliyan ɗaya da dubu ɗari kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

Kara karanta wannan

Masanin Tattalin Arziƙi Ya Fadi Abinda Zai Faru Idan Ministocin Tinubu Suka Fara Aiki

An gurfanar da matashi gaban kotu kan zargin sata a maƙabarta
An maka matashin gaban ƙuliya bisa zargin sata a maƙabarta a Legas. Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Yadda matashin ya tafka sata a maƙabarta

Ana tuhumar matashin Mubarak Kajola da ba a bayyana inda yake da zama ba da laifuka uku; keta haddi, sata da kuma ta'ammuli da miyagun makamai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami'a mai gabatar da ƙara Funmi Akinleye, ta shaidawa kotun cewa wanda ake zargi ya shiga maƙabarta ba bisa ƙa'ida ba tare da keta haddin mamatan da ke kwance a cikinta.

Ta ce a ranar Juma'a 11 ga watan Agusta ne wanda ake zargin ya shiga cikin maƙabartar sannan ya sace ƙarafan da ake rufe gawa da su da kuɗinsu ya kai naira miliyan 1.1.

Matashin yana ɗauke da makami a lokacin da yake satar

Misis Akinleye ta kuma shaidawa kotun cewa, matashin na ɗauke da wata bindiga a lokacin da ya je tafka wannan mummunar ta'asa a maƙabartar.

Ta kuma bayyana cewa laifukan da matashin ya aikata sun ci karo da sashe na 165 (b), 280(1), 287, 312 da 312(a)(b) na kundin hukunta manyan laifuka na Najeriya kamar yadda Peoples Gazette ta wallafa.

Kara karanta wannan

Jami'an Hukumar Kwastam Sun Kama Harsasai 1,245 Da Aka Boye Cikin Buhunan Shinkafa 'Yar Waje

Mai shari'a Oyenike Fajana, ta ba sa da umarnin a tsare wanda ake tuhuma a gidan gyaran hali na kiri-kiri da ke Legas, sannan ta ɗage sauraron shari'ar zuwa 17 ga watan Agusta.

Barau ya nemi a taya su addu'a kan shari'ar Abba da Gawuna

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan roƙon da mataimakin shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Sanata Barau Jibrin Maliya ya yiwa 'yan Najeriya dangane da shari'ar Abba Gida Gida da Gawuna na jihar Kano.

Barau ya nemi 'yan Najeriya da su taya su da addu'ar samun nasarar ƙwace kujerar gwamnan Kano da Injiya Abba Kabir Yusuf na NNPP ke shugabanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng

Online view pixel