Masu Ruwa Da Tsaki A APC Sun Roki Tinubu Ya Sauya El-Rufai Daga Kudancin Kaduna

Masu Ruwa Da Tsaki A APC Sun Roki Tinubu Ya Sauya El-Rufai Daga Kudancin Kaduna

  • Kungiyar masu ruwa da tsaki a jam'iyyar APC ta jihar Kaduna ta roki Tinubu kan na da minista daga Kudancin Kaduna
  • Ta ce ganin yadda Nasir El-Rufai ya ajiye mukamin minista, zai fi kyau a duba bangaren Kaduna ta Kudu a yanzu
  • Ibrahim Koli, shugaban APC na karamar hukumar Jema'a a jihar shi ya bayyana haka a madadin kungiyar a cikin wata sanarwa

FCT, Abuja - Masu ruwa da tsaki a jam'iyyar APC mai mulki a jihar Kaduna sun bukaci Shugaba Tinubu ya zabo minista daga Kudancin Kaduna.

Wannan na dauke ne a cikin wata sanarwa da shugaban jam'iyyar APC na karamar hukumar Jema'a, Ibrahim Koli ya sanya wa hannu.

APC ta bukaci Tinubu ya maye gurbin El-Rufai daga Kaduna ta Kudu
Jam'iyyar APC Ta Roki Tinubu Ya Sauya El-Rufai Daga Kaduna Ta Kudu. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Me APC ta ce kan mukamin El-Rufai?

Ya ce bisa ga alamun cire sunan Nasir El-Rufai, ya fi kyau a dauko madadin shi daga Kudancin Kaduna don samun daidaito.

Kara karanta wannan

DSS: ‘Yan Ta’adda Sun Yi Shirin Kai wa Mutane Mugun Hari a Jirgin Abuja-Kaduna

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

"Wannan kungiya da ta kunshi tsoffin shugabannin kananan hukumomi da masu ci da kuma manyan masu mukami a APC muna kira ga Tinubu da ya dauko minista daga Kudancin Kaduna.
"Ganin yadda tsohon gwamnan jihar, Nasiru El-Rufai ya ajiye neman kujerar minista da kansa, zai fi kyau a dauko madadinshi daga wannan yanki.
"Abin takaici ne yadda kowa ya goyi bayan El-Rufai a kan kujerar ministan, amma kuma yanzu ya ki amincewa da tayin."

Koli ya ce a Kudancin Kaduna su na da mutane jajirtattu da za su rike wannan kujera ta minista, cewar Vanguard.

Da waye su ke son a maye El-Rufai?

Koli ya ce:

"Mu na roko a sake ba mu dama a Kudancin Kaduna wanda mu ka rasa tun hawan gwamnatin APC a 2015.
"Mu na da jajirtattu kamar Dakta Abdulmalik Dogonruwa wanda shi ne kwamishinan Tarayya na hukumar kidaya.

Kara karanta wannan

Shari'ar Gwamnan Kano: Mataimakin Shugaban Majalisa Ya Roki Yan Najeriya Su Taya APC Addu'ar Samun Nasara Kan PDP

"Dogonruwa na da kwarewa matuka a fannin aiki da kuma irin gudumawa da ya bayar a zaben 2023 da ya gabata a Kudancin Kaduna."

Ibrahim ya ba wa shugaban kasa, Bola Tinubu tabbacin cewa ba zai yi dana sanin na da Dogonruwa minista ba, cewar Leadership.

El-Rufai Ya Hakura Da Mukamin Minista

A wani labarin, Malam Nasiru El-Rufai ya ce ba ya sha'awar zama minista a gwamnatin Tinubu.

El-Rufai ya ajiye mukamin ne bayan cikas da aka samu yayin tantance shi a majalisa inda ya ce yana da wanda zai maye gurbinshi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel