Latest
Wata babbar kotu a jihar Ribas ta hana majalisar dokokin jihar tsige Gwamna Siminalayi Fubara. An dai samu rikicin siyasa a jihar Rivers cikin kwanakin nan.
Wasu masu zanga-zanga sun yi tattaki har zuwa zauren majalisar tarayya da ke Abuja ranar Laraba, sun buƙaci a tsige Bello Matawalle daga matsayin ministan tsaro.
Hukumar EFCC ta samu nasarar cafke dalibai 69 bisa zargin aikata laifukan damfara ta intanet inda ta kwace motoci, wayoyi 190 da kuma kwamfutoci 40.
Mambobin ƙungiyar gwamnonin babbar jam'iyyar adawa ta ƙasa PDP karkashin jagorancin Gwamna Bala Muhammed na Bauchi sun shiga ganawa da ministan Abuja.
Majalisar dattijan Najeriya ta tantance tare da tabbatar da naɗim sabbin kwamishinonin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC a zaman yau Laraba.
A ranar Laraba, majalisar dattawan Najeriya ta amince da dala biliyan 7.8 da kuma yuro miliyan 100 a matsayin kudin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai ciyo bashi.
Kungiyar Kwadago a Najeriya, NLC ta tura sakon gargadi ga gwamnati kan kame shugabanta, Joe Ajaero, ta ce za ta durkusar da Najeriya da yajin aiki.
Bola Ahmed Tinubu ya halarci taron da ake yi wa mukarrabansa da jami’an gwamnati, a nan ya ce duk wani wanda ba zai iya sauke nauyin ba, ya ajiye aikinsa.
Ministan harkokin birnin tarayya na Abuja, Nyesom Wike ya yi karin haske a kan abin da ya haddasa rigimar siyasar da ake fama da ita a halin yanzu a Ribas.
Masu zafi
Samu kari