Kungiyar NLC ta tura gargadi daya rak ga gwamnati da zai dagula kasar, ta bayyana dalili

Kungiyar NLC ta tura gargadi daya rak ga gwamnati da zai dagula kasar, ta bayyana dalili

  • Kungiyar Kwadago ta NLC ta zargi Gwamna Hope Uzodinma da jami'an 'yan sanda da garkuwa da shugabanta
  • Kungiyar ta yi gargadi mai tsauri ga gwamnati da ta sake shugabanta ko kuma ta durkusar da kasar da yajin aiki
  • Wannan na zuwa ne yayin da jami'an tsaro su ka kama Joe Ajaero yajin gudanar da zanga-zanga a Owerri babban birnin jihar Imo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kungiyar Kwadago ta NLC, ta yi martani bayan kame shugabanta, Joe Ajaero a jihar Imo.

Kungiyar ta ce idan har gwamnati ba ta saki Ajaero za ta durkusar da kasar da yajin aikin gama-gari.

Kungiyar NLC ta tura gargadi ga gwamnati kan kama Ajaero
Kungiyar NLC ta tura gargadi ga gwamnati kan shugabanta. Hoto? NLC.
Asali: Twitter

Wane gargadi NLC ta yi kan kame Ajaero?

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da aka kwashi shugaban NLC Ajaero zuwa asibiti, cikakken bayani

Kungiyar ta ce daga yanzu zuwa karfe 12 na dare idan har ba ta samu abin da ta ke so ba, komai na iya faruwa a kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan gargadi na zuwa ne bayan kame shugaban kungiyar a jihar Imo yayin gudanar da zanga-zanga a birnin Owerri na jihar, cewar Vanguard.

Kungiyar na takun-saka da gwamnati kan inganta rayuwar 'yan kasa da kuma rage radadin wahalar da ake ciki a kasar tun bayan cire tallafin mai.

Mene kungiyar NLC ke cewa kan kama Ajaero?

A cikin wata sanarwar da kungiyoyin NLC da TUC su ka fitar, sun zargin Gwamna Hope Uzodinma da 'yan sanda da yin garkuwa da Ajaero.

Kungiyar ta kara da cewa babu yadda za a yi ma'aikata su yi aiki yayin da shugabansu ke garkame a komar jami'an'yan sanda.

Kara karanta wannan

Rundunar 'yan sanda: Abin da yasa jami'anmu suka watsa wa gwamna ruwan zafi da barkonon tsohuwa

A wannan makon ne kungiyar NLC ta gargadi ministan kwadago, Simon Bako Lalong da kada ya kuskura ya halarci taron da za ta tattauna da gwamnati.

Jami'an tsaro sun cafke shugaban NLC, Ajaero

A wani labarin, rundunar 'yan sanda sun cafke shugaban kungiyar kwadago ta kasa, NLC, Joe Ajaero a jihar Imo.

An kama Ajaero ne a yau Laraba 1 ga watan Nuwamba yayin gudanar da zanga-zanga a sakatariyar kungiyar a Owerri.

Wannan na zuwa ne bayan takun-saka da ake yi tsakanin kungiyar da Gwamnatin Tarayya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel