Tinubu: Duk Minista Ko Wani da Ba Zai Iya Tabuka Komai Ba, Ya Tafi Ya Ba Ni Wuri

Tinubu: Duk Minista Ko Wani da Ba Zai Iya Tabuka Komai Ba, Ya Tafi Ya Ba Ni Wuri

  • Bola Ahmed Tinubu ya halarci taron da ake yi wa mukarrabansa, ministoci, hadimai da kuma jami’an gwamnatin tarayya
  • Shugaban kasar ya ce duk wani wanda ba zai iya sauke nauyin da yake wuyansa ba, abin da ya dace shi, shi ne ajiye aikinsa
  • Mai girma Tinubu ya bukaci ministocin da ya rantsar da sauran wadanda aka ba mukamai su yi kokarin fitar da shi kunya

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Duk wanda aka ba mukami ko jami’in gwamnatin tarayya da ba zai iya sauke nauyin da ke wuyansa ba, kofa a bude ta ke ya yi gaba.

A ranar Talata, Daily Trust ta rahoto Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya na cewa dole ya yi bakin kokarinsa ya biyawa ‘yan Najeriya bukatunsu

Kara karanta wannan

Wike ya karyata rade-radi, ya shaidawa Gwamnoni silar rigimarsa da Gwamnan Ribas

Saboda haka shugaban kasar ya ce kofarsa a bude ta ke ga wanda aka ba matsayi ko mukami, sai ya ga ba zai iya aikin da aka daura masa ba.

Bola Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Tinubu da mukarrabansa Hoto: @Dolusegun
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana yi wa Ministoci da Mukarraban Tinubu bita

Bola Tinubu ya yi wannan magana da yake jawabi wajen taron kwanaki uku da aka shiryawa Ministoci, hadimai da manyan jami’an gwamanti.

Rahoton ya ce ana yi wa mukarraban shugaban kasa da manyan gwamnatin tarayya bita.

Bola Tinubu ya tabbatar masu cewa zai ba kowa damar yin aikinsa da kyau, ya kuma ba su shawarar yin tambaya kan yadda za su bullowa aikinsu.

Shawarwarin da Shugaba Tinubu ya bada

A jawabinsa, Mai girma Tinubu ya zaburar da wadanda ke wajen taron da su dage domin cin ma nasara,ya na mai tuna masu kowa ya na kuskure.

Kara karanta wannan

Wani fasto mai tsala-tsalan mata 2 kuma yake shirin auren ta 3 ya hakura, ya fadi dalili

Da zarar ‘dan adam ya yi kuskure, abin da ake bukata shi ne ya yi maza ya gyara, a cewar Tinubu, jami’an su na kujerunsu ne domin taimaka masa.

Shawarar da shugaban kasar ya ba jami’an gwamnati shi ne su daina kallon Ministoci a a wadanda za su bar kujerunsu, su bar su a gwamnati.

Su kuwa Ministocin, an tunatar da su cewa dama su ka samu da za su bautawa kasarsu, don haka su dage wajen yin aikin da zai taimaki Najeriya.

Tinubu ya ce ya gaji alherai da sharrin gwamnatin baya, kuma ya yi kira ga masu hannun jari.

Gwamnonin PDP sun yabi Tinubu

Dazu aka ji labari cewa 'yan kungiyar Gwamnonin PDP sun yi taro a Abuja inda su ka yabi yadda Bola Tinubu ya hana ayi waje da Gwamnan jihar Ribas.

Bala Mohammed, Siminalayi Fubara, Ahmadu Umaru Fintiri, Ademola Adeleke, Sheriff Oborevwori da wasu gwamnonin jihohi su ka halarci taron.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel