Da Duminsa: Makusancin Buhari, Tsohon Kakakin CPC Kuma Darakta a NIMASA, Ya Kwanta Dama

Da Duminsa: Makusancin Buhari, Tsohon Kakakin CPC Kuma Darakta a NIMASA, Ya Kwanta Dama

  • Makusancin shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma tsohon daraktan ayyuka na hukumar NIMASA, Rotimi Fashakin ya kwanta dama
  • Kafin rasuwarsa, ya taba kasancewa kakakin tsohuwar jam'iyyar CPC kuma jigon jam'iyyar APC a halin yanzu
  • Ya rasu a birnin Landan inda yake karatun shari'a a jami'ar Buckingham kuma zai kammala a watan Disamban 2022

Tsohon daraktan ayyuka na Nigerian Maritime Administration and Safety Agency (NIMASA), Injiniya Rotimi Fashakin, ya kwanta dama yayin da yake karatun sharia'a a Ingila.

Jigon jam'iyyar APC din ya kasance tsohon kakakin tsohuwar jam'iyyar Congress for Progressive Change (CPC), Daily Trust ta rahoto.

Fashakin
Da Duminsa: Makusancin Buhari, Tsohon Kakakin CPC Kuma Darakta a NIMASA, Ya Kwanta Dama. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Har ila yau, yayi aiki a matsayin zababben daraktan NIMA daga 2016 zuwa watan Maris sin 2022, ya rasu kwatsam a yammacin ranar Asabar a Landan.

Kafin rasuwar Fashakin, dalibi ne mai karantar fannin shari'a a jami'ar Buckingham kuma zai kammala karatunsa a watan Disamban 2022.

Kara karanta wannan

2023: Rawar Da Nake Takawa Na Kawo Karshen Rikicin Atiku da Wike a Sirrince, Saraki Ya Magantu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mamacin ya kammala digirinsa a jami'ar Ife wacce a yanzu ta koma jami'ar Obafemi Awolowo ta Ile-Ife, jihar Osun inda ya karancin fannin wutar lantarki.

Makusancinsa, Eyitayo Ajayi, ya tabbatar da mutuwar 'dan siyasan a wallafar da yayi a shafinsa na Facebook.

"Na yi rashin 'dan uwa Injiniya Rotimi Fashakin a daren jiya. Ina fatan Ubangiji ya bai wa iyalansa hakurin jure rashinsa."

- Yace a wallafar.

Mamacin ya rasu ya bar matar aure daya mai suna Olubusola da 'ya'ya.

Mata Tayi Shigar Ma'aikatan Lafiya, Ta Sace Daya Daga Cikin Tagwayen da Aka Haifa a Asibiti

A wani labari na daban, an shiga tashin hankali a dakin haihuwa na asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, inda aka sace daya daga cikin tagwaye da aka haifa.

A zantawarsa mahaifin tagwayen da aka haifa da Daily Trust, Ibrahim Dallami Khalid ya ce wata mata ta shiga dakin da matarsa take kwance ​​da tagwayen a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Wutar Lantarki Ta Dauke A Najeriya Gaba Daya Da Safiyar Nan, 0 Megawatt

Asali: Legit.ng

Online view pixel