Kungiyar 13x13: Bayan tsawon lokaci, anga bidiyon Tsohuwar Jaruma Rahama Hassan a kungiyar Kannywood

Kungiyar 13x13: Bayan tsawon lokaci, anga bidiyon Tsohuwar Jaruma Rahama Hassan a kungiyar Kannywood

  • Shahararriyar tsohuwar jarumar Kannywood, Rahama Hassan ta dawo cikin masana'antar
  • Sai dai a wannan karon Rahama ta dawo ne a matsayin mamba ta kungiyar 13X13 ba wai a matsayin jarumar fim ba
  • An dai dauki tsawon lokaci ba a ji doriyar jarumar ba har zuwa lokacin da ta yi aure, inda aka daina jin labarinta ko a soshiyal midiya

Shahararriyar tsohuwar jarumar masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Rahama Hassan ta dawo cikin abokan sana’arta bayan dogon lokaci.

Tun kafin jarumar ta yi aure ba’a kara jin doriyarta ba a masana’antar ta shirya fim harma ga shafukan soshiyal midiya.

Kungiyar 13x13: Bayan tsawon lokaci, anga bidiyon Tsohuwar Jaruma Rahama Hassan a kungiyar Kannywood
Kungiyar 13x13: Bayan tsawon lokaci, anga bidiyon Tsohuwar Jaruma Rahama Hassan a kungiyar Kannywood Hoto:hutudole.com/youtube
Asali: UGC

Kwatsam yanzu sai ga wasu bidiyonta sun bayyana a shafukan sadarwar zamani sanye da hular 13X13 kuma cikin mambobin kungiyar nan ta 13X13.

Kara karanta wannan

Kano: Mummunar gobara ta lamushe kadarorin N18m a Mariri

13×13 kungiya ce da ta hada fitattun manyan fasihan mawakan Kannywood, wadanda su ne kashin bayan tafiyar, sannan akwai fitattun daraktoci, furodusoshi da kuma ‘yan wasa da sauran su a cikinta.

Harma akwai wani bidiyo da babban furodusa Mallam Abubakar Bashir Maishadda ya wallafa a shafinsa na tiktok dauke da rubutun ‘Rahama Hassan is back’ wato Rahama Hassan ta dawo.

Rahama bata dawo fim ba, mamba ce a kungiyar 13X13 - Maishadda

Sai dai da wakiliyar Legit Hausa ta tuntube shi don jin ko da gaske Rahama Hassan ta dawo harkar fim, Maishadda ya tabbatar da kasancewar jarumar a cikin kungiyar ta 13X13 amma ya ce bata dawo harkar fim ba.

Maishadda ya ce:

“Bata dawo fim ba amma mamba ce a kungiyar 13X13.”

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Matasan APC a arewa za su siyawa Umahi fam din takara

Ga bidiyon nata a taron kungiyar:

Mutane su gama aibatani a zo ranar lahira su ga na shige Aljanna na barsu - Umma Shehu

A wani labarin, Shahararriyar jarumar masana’antar shirya fina-finan hausa ta Kannywood ta yi tsokaci a kan aibata ta da wasu mutane ke yi, sakamakon kallo da suke yi mata a matsayin mai aikata sabon Ubangiji.

A wani bidiyo da sashin Hausa na BBC ya fitar, an jiyo jarumar tana fadin cewa ita da zunubinta ta damu ba da na wani ba sannan kuma cewa duk a laifukan da take aikatawa bata hada Allah da wani.

Jarumar ta kuma bayyana cewa tana cika salollinta guda biyar, don haka Allah mai gafara ne, idan ta roke sa cikin kuka zai yafe mata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel