Bidiyon katafaren gidan bene na alfarma da jaruma Rukayya Dawayya ta gina wa kan ta

Bidiyon katafaren gidan bene na alfarma da jaruma Rukayya Dawayya ta gina wa kan ta

  • Jaruma Rukayya Dawayya ta kammala gina wani katafaren gidan bene na kanta a cikin birnin Kano
  • Jarumar ta wallafa bidiyon ciki da wajen katafaren ginin a shafinta na Instagram amma cikin mintuna kadan ta goge
  • Sannannen abu ne cewa jarumar ta dade a masana'antar kuma 'yar kasuwa ce domin da kudinta ta shigo harkar fim

Kano - A kwanakin baya jaruma Rukayya Dawayya ta fara gina wani tamfatsetsen gida a Kano wanda da ganinsa ka san an yi barin miliyoyin naira wajen gina shi.

Tun ana tsaka da ginin gidan ta wallafa a shafinta na Instagram inda abokan sana'arta suka dinga taya ta murna da fatan kammalawa lafiya.

A halin yanzu dai wannan katafaren gida ya kammalu inda ta sake wallafa bidiyon ciki da wajensa a shafinta na Instagram tare da mika godiya ga Allah da ya bata ikon kammala ginin nata.

Kara karanta wannan

Yadda Zainab Ta Gutsure Kunnen Masoyinta Saboda Ya Ba Ta N365 Matsayin Kuɗin Mota

Bidiyon katafaren gidan bene na alfarma da jaruma Rukayya Dawayya ta gina wa kan ta
Bidiyon katafaren gidan bene na alfarma da jaruma Rukayya Dawayya ta gina wa kan ta. Hoto daga @dawayyarukayya85
Asali: Instagram

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai ko da jarumar ta wallafa bidiyon a shafinta, babu jimawa ta goge wanda za ta yuwu hakan ya na da alaka da irin maganganun da za ta iya samu a sashin tsokaci ne.

Legit.ng ta lalubo muku bidiyon daga shafin masana'antar a Instagram inda aka wallafa tare da taya ta murna.

A cikin kwanakin nan an dinga kai ruwa rana da matan masana'antar bayan jaruma Ladin Cima ta bayyana cewa dubu biyu zuwa dubu biyar ake biyansu wurin daukar fim.

A lokacin ne Rukayya Dawayya ta sanar da cewa basu dogara da fim ba domin suna sana'o'i da tallukan kamfani da sauransu.

Amma ko da ganin wannan katafaren gidan, ka san da wahala fim ko talluka su gina shi. Sai dai sanin kowa ne jarumar ta dade a masana'antar kuma ko sanda ta zo da kudinta ta bayyana haka ma iyayenta na da rufin asiri sannan yanzu haka 'yar kasuwa ce.

Kara karanta wannan

Bidiyon Wata 'Yar Najeriya Da Ta Gano Ashe 'Yar Aikinta Gardi Ne Bayan Wata 3, Ta Tozarta Shi

Babu dan fim da ya tumbatsa duniya ta san shi da zai ce iya kudin fim ke rike shi – Rukayya Dawayya

A wani labari na daban, shahararriyar jarumar masana’antar Kannywood, Rukayya Umar wacce aka fi sani da Dawayya ta yi martani a kan cece-kucen da mutane ke yi game da inda manyan jarumai musamman mata ke samun kudin da suke fantamawa bayan Ladin Cima ta ce ana biyanta N2,000.

Da farko dai jarumar ta ce ko daya bata ji haushin abun da Baba Tambaya tayi ba domin a cewarta ta taso a hannun dattijai kuma ta san basa kiran kudade da yawa idan suna magana.

Ta kuma bayyana cewa ta yiwu dattijuwar jarumar ta rude ne yayin da aka yi mata tambayar domin a cewarta ba wai a kan fada ma mutum abun da za a tambaye shi a kai bane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel