Bidiyon Wata 'Yar Najeriya Da Ta Gano Ashe 'Yar Aikinta Gardi Ne Bayan Wata 3, Ta Tozarta Shi

Bidiyon Wata 'Yar Najeriya Da Ta Gano Ashe 'Yar Aikinta Gardi Ne Bayan Wata 3, Ta Tozarta Shi

  • Wata ‘yar Najeriya ta dauki ‘yar aiki mace wacce ta kwashe watanni uku tana yi mata hidima, sai daga baya ta gano abinda ya firgita ta akan ta
  • Matar ta sha mamaki bayan gano ashe katon namiji ne ‘yar aikin nata inda ta yi masa bidiyo tare da fallasa shi a idon duniya don kowa ya sani
  • Nan da nan mutanen da suka ga faruwar lamarin ta hanyar duba bidiyon ‘yar aikin suka dinga tsokaci iri-iri kowa da nasa ra’ayin

Ki kwatanta daukar ‘yar aiki kawai sai ki gano cewa ta daban ce da wacce ta bayyana miki a zahiri, to irin haka ne ya faru da wata ‘yar Najeriya.

Matar wacce sunanta bai bayyana ba ta gano cewa wacce ta dauka aiki daban da wacce take yi mata aiki, don namiji ne ba mace ba.

Kara karanta wannan

Kyakkyawan Matar Aure Ta Saki Bidiyon Mijinta Yana Musu Girki Cikin Nishaɗi A Gida, Tace Ba Za Ta Koka Ba

Bidiyon Wata 'Yar Najeriya Da Ta Gano Ashe 'Yar Aikinta Gardi Ne Bayan Wata 3, Ta Tozarta Shi
Yar Najeriya Da Ta Gano Ashe 'Yar Aikinta Gardi Ne Bayan Wata 3, Ta Tozarta Shi. Hoto: @ourtalkroom
Asali: Instagram

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

@ourtalkroom ta wallafa bidiyon yadda matar ta kunyatar da mai aikin inda tace sai da ta kwashe watanni uku tana yi mata aiki sannan ta gano gaskiya.

Ya kunyata matuka a bidiyon

Ya sha kunya a bidiyon, inda ka ga yadda dan aikin yake zaune a kasa sanye da rigar mama da wani wandon jins. Ya sanya hular gashi kuma.

Daga bisani aka sanya hadimin a cikin abin hawa wanda alamu suna nuna kamar ofishin ‘yan sanda aka zarce da shi.

Abin ban mamakin shi ne yadda dan aikin ya kwashe watanni uku yana aiki ba tare da asirin sa ya tonu ko kuma ya yi kuskuren da zai sa a gano shi ba.

Ga bidiyon a kasa:

Tsokacin jama’a karkashin wallafar

@bonny_noni ya ce:

“Akalla bai yi mata sata ko kuma tsafi ba, mutumin yana bukatar kudi ne kuma samun aiki ba wasa bane.”

Kara karanta wannan

Aure Daɗi: Bidiyon Yadda Wata Mata Ta Maƙale Wa Mijinta, Ta Hana Shi Rawar Gaban Hantsi

@laureldoll ya ce:

“Kila yana bukatar aiki ne ido rufe don tallafa wa rayuwarsa shiyasa ya tsaya a matsayin mace. Amma dai ban ga laifin sa ba. Da wani wurin ne da ya ci bakin duka.”

@zayne_ryker ya yi tsokaci da:

“Amma in har ya boye don ya samu aiki, matsawar ba cutar da ke yake yi ba, na tsawon watanni uku ba tare da ya yi yunkurin cutar da ke ba, bai dace ki wulakanta shi ba."

@absolut_shuga ya yi tsokaci inda ya ce:

“Cikin abubuwa biyu akwai daya, ko dai bukatar aikin ne yasa ya boye gaskiya dangane da shi ko kuma yana da wata manufa.”

An sha mamaki bayan gano cewa gardin namiji aka tura gidan yari na mata ba tare da an gane a kotu ba

A wani labarin, wani lamari mai ban mamaki ya auku a gidan gyaran halin mata da ke Shurugwu inda aka gano wata fursuna ba mace bace, katon namiji ne kamar yadda LIB ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Duk da Kyauna, “Samarin Shaho” Guduna Suke yi, Budurwa Mai Kamun Kai Tayi Bayani

Praise Mpofu mai shekaru 22 ya na sanye da suturar mata ne a lokacin da aka kama shi inda ya bayyana kamar karuwa don ya yaudari maza ya yi musu sata.

An kama Mpofu ne bayan ya yi wa wani mutum da ke yankin Gweru sata. An samu rahoto akan yadda mutumin ya caskewa Mpofu kudi don su kwana tare da shi a tunanin sa mace ne, daga nan Mpofu ya yashe shi ya tsere.

Asali: Legit.ng

Online view pixel