Yadda Zainab Ta Gutsure Kunnen Masoyinta Saboda Ya Ba Ta N365 Matsayin Kuɗin Mota

Yadda Zainab Ta Gutsure Kunnen Masoyinta Saboda Ya Ba Ta N365 Matsayin Kuɗin Mota

  • Zainab Ochero da mijin ta, Joseph Karanja sun hadu don tattaunawa tsakanin su akan matsalolin da suke fuskanta na auren su
  • Sun kasa daidaitawa da junayensu bayan Karanja ya zarge ta da yin lalata da wasu mazan banza wanda hakan ne ya fi fusata ta
  • Lamarin ya hassala Ochero inda ta kara fusata bayan Karanja ya ba ta N365 don ta yi kudin motar komawa gida, cikin fushi ta cije masa kunne daya

An gurfanar da wata mata ‘yar Kawangware, yankin Nairobi bisa rikici akan yadda ta cizge kunnen mijinta har ta kai ga kunnen ya cire.

Ana zargin Zainab da yin aika-aikar ne bayan masoyin nata, Joseph Karanja ya ba ta KSh 100, wato N365 a matsayin kudin mota don ta koma gida.

Kara karanta wannan

Bidiyon katafaren gidan bene na alfarma da jaruma Rukayya Dawayya ta gina wa kan ta

Yadda Mata Ta Gutsure Kunnen Masoyinta Bayan Mutumin Ya Ba Ta N365 Matsayin Kudin Mota
Mata Ta Gutsure Kunnen Masoyinta Bayan Ya Ba Ta N365 Matsayin Kudin Mota. Hoto: Clause Masika
Asali: UGC

Ta fadi kasa tana rokon alkali

Ta fadi kasa gaban alkalin kotun majistaren Kiber, Charles Mwaniki a ranar Talata, 1 ga watan Maris, inda ta musanta ji wa Karanja mummunan raunin a yankin Kangemi da ke Nairobi a ranar Litinin, 21 ga watan Fabrairu, Nairobi News ta ruwaito.

Rahoton ‘yan sanda ya bayyana yadda cikin fushi matar ta kama mutumin ta gannara wa kunnensa na hagu cizo har sai da ta cire shi ya fadi kasa.

Bayan ganin kunnen ya fadi kasa, Karanja ya yi gaggawar dauka inda ya sanya a leda inda ya zarce asibiti don samun kulawar likita.

Daga nan aka tura shi wani asibiti da ke Eastland inda aka sanar da shi cewa an cizge kunnen da gangan wanda ya janyo lalacewar shi, kuma sai an yi masa aiki na musamman wanda zai dauki watanni 3 kafin ya warke.

Kara karanta wannan

Sai Miji Na Ya Lakaɗa Min Baƙin-Duka Sannan Yake Kwanciya Da Ni, Mata Ta Nemi Saki a Kotu

Sun zauna ne don tattaunawa akan matsalolin su na cikin gida

Tun farko sun zauna don su tattauna a wani wuri don su fuskanci juna bayan Karanja ya zarge ta da lalata da mazan banza.

Ba su samu damar daidaitawa ba har abin ya koma musu fada, daga nan Ochero ta tsayar da babur wanda zai mayar da ita gida a Kawangware.

Anan ne Karanja ya mika mata KSh 100 wato N365 don ta yi kudin babur da shi.

Dama a fusace take bisa zargin da ya yi mata sai kuma ga kudin babur din da ya bata, daga nan Ochero ta gannara wa kunnen Karanja cizo.

Citizen Digital ya ruwaito yadda Mwaniki ya bayar da umarnin a sake ta amma sai ta biya KSh 300,000 wanda ya yi daidai da N1,000,000 sannan an dage sauraron karar zuwa ranar Laraba, 16 ga watan Maris.

Mata ta ‘yar bala’i ce, da adda take bi na: Wani mutum ya bukaci kotu ta raba shi da matarsa

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Gobara ta sake kaca-kaca da sansanin yan gudun hijira a Borno

A wani labarin, Legit.ng a rahoto cewa Mr Steve Bashorun mai shekaru 61 ya maka matarsa Oluwaseyi, gaban kotun Alagbado da ke Jihar Legas ranar Alhamis bisa zargin ta da yunkurin halaka shi, Vanguard ta ruwaito.

Steve wanda mazaunin yankin Ikola ne ya sanar da yadda suka kwashe shekaru 17 da auren matarsa mai shekaru 40.

Ya zarge ta da kin kulawa da yaran su uku tare da wulakanta dangin sa musamman mahaifiyarsa, kafin ta rasu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel