Babu dan fim da ya tumbatsa duniya ta san shi da zai ce iya kudin fim ke rike shi – Rukayya Dawayya

Babu dan fim da ya tumbatsa duniya ta san shi da zai ce iya kudin fim ke rike shi – Rukayya Dawayya

  • Jarumar Kannywood, Rukayya Dawayya ta yi martani a kan cece-kucen da mutane ke yi game da inda manyan jarumai musamman mata ke samun kudin da suke fantamawa
  • Hakan ya biyo bayan furucin da abokiyar sana'arta Ladin Cima ta yi na cewa ana biyan N2,000 a shirin fim
  • Dawayya ta ce suna samun kudinsu ne ta hanyar talulluka, jakadanci, talullukan siyasa, kwangila, kasuwanci da dai sauransu

Shahararriyar jarumar masana’antar Kannywood, Rukayya Umar wacce aka fi sani da Dawayya ta yi martani a kan cece-kucen da mutane ke yi game da inda manyan jarumai musamman mata ke samun kudin da suke fantamawa bayan Ladin Cima ta ce ana biyanta N2,000.

Da farko dai jarumar ta ce ko daya bata ji haushin abun da Baba Tambaya tayi ba domin a cewarta ta taso a hannun dattijai kuma ta san basa kiran kudade da yawa idan suna magana.

Kara karanta wannan

Ni 'yar Drama ce, 'yar Nanaye, ina alfahari da hakan, Maryam Booth

Babu dan fim da ya tumbatsa duniya ta san shi da zai ce iya kudin fim ke rike shi – Rukayya Dawayya
Dawayya ta ce suna samun kudadensu ne ta hanyar talulluka da sauransu Hoto: dawayyarukayya85
Asali: Instagram

Ta kuma bayyana cewa ta yiwu dattijuwar jarumar ta rude ne yayin da aka yi mata tambayar domin a cewarta ba wai a kan fada ma mutum abun da za a tambaye shi a kai bane.

Sannan game da inda suke samun kudaden da suke hawa manyan motoci da gidaje, Dawayya ta ce duk wani jarumi da ya shahara kudin fim kadai ba zai iya rike shi ba, inda ta ce suna samun kudadensu ta hanyar talulluka, jakadanci, talullukan yan siyasa da kuma kwangila.

Ta wallafa a shafinta na Instagram cewa:

“Tun jiya da bidiyon Mama Tambaya ya fita mutane na ta tagin dina, toh tace ba a biyan kudi ku ina kuke samun kudi ku ke gidaje, ku ke motoci. Ni da na ga bidiyon Mama Tambaya wallahi bai bani haushi ba. Saboda ni ina tare da iyayena tunda na tashi dama ina tare da dattijai irin su Mama Tambaya.

Kara karanta wannan

Karon farko sun hau jirgi: Martani yayin da budurwa ta share wa iyayenta hawaye

“Don haka ni nasan yaren kudi yadda mu manyanmu suke yi, cikin dattako suke yin shi. Basa kiran kudi da yawa sai dai dan kadan kuma maganar makudan kudi ake yi.
“Magana ta biyu ta yiwu ta rude ne tana gaban yan jarida wanda ta yiwu basu fada mata abun da za su tambaye ta a kai ba. Kuma ni ina jin dadin shirin nan na BBC amma wani lokacin basa fada ma mutum ga abun da za mu tambaye ka a kai, sai dai idan kai ka tambaye su a kan me za ku tambayeni.
“Wata kila kawai sun jefo mata tambaya ita kuma sai wannan kawai ya fado bakinta, amma sai ba a duba alkhairin da ta fada ba sai wannan Kalmar ita ce take ta yawo. Su kuma mutane dama wadansun su suna hassada da mu, suna bakin ciki da mu, shiyasa duk motsinmu sai an ce nawa ake samu a fim din kuke kaza kuke kaza, toh sai kuma gashi wannan magana ta fito daga Baba Tambaya.

Kara karanta wannan

Sauki ya samu: Sabbin hotuna da bidiyon Maryam Yahaya a kasar Dubai

“Duk duniya babu inda wani da ya shahara ya riga ya tumbatsa duniya ta san da shi, yayi suna kuma ace iya abun da ake biyansa a fim ne yake rike shi, babu shi. Talulluka da ake yi, jakadanci da ake yi, talullukan yan siyasa, kwangilan da ake ba wasu daga ciki, wasun su kuma suna kasuwanci, ba sai an fito ance maku ga shagona ba. Wasu daga cikin yan fim wallahi kasuwancin da suke yi kanku ba zai dauka ba.
“Wasu shaguna da kasuwanci da kuke gani na yan Kannywood ne. amma dama nawa ake biya a fim, duk abun da ake biya a fim ba za ki je ki siya mota da shi ko gida da shi ba, amma za a baki iya abun da za a baki, amma maganar N2,000 babu ita. Jama’a ku fassara wannan kudin maganar kudade masu yawa.”

Batun lalata da matan fim: Nafisa Abdullahi ta saki martani ga Sarkin waka

Kara karanta wannan

Naziru sarkin waka ya yiwa Ladin Cima da Fati Slow kyautan miliyoyi naira

A gefe guda, kamar yadda Legit.ng ta gano, batun da yafi yi wa 'yan Kannywood zafi a maganar sarkin waka shi ne batun lalata da mata kafin a saka su a fim inda matan Kannywood ke ta fitowa suna musanta waccan maganar da yayi.

Jaruma Nafisa Abdullahi ta rubuta budaddiyar wasika cikin harshen turanci a shafinta na Instagram kuma ta kara da bayani a kasan wasikar da harshen Hausa inda ta bayyana cewa babban zargi ya fitar tunda ta na cikin matan masana'antar.

Jarumar ta yi kira ga sarkin wakan idan ya na da matsala da wani ne, ya bayyana sunansa su yi ta kare ba wai ya bata masana'antar ba baki daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel