Ayiriri: Jaruma Aisha Aliyu Tsamiya za ta shiga daga ciki a ranar Juma'a mai zuwa

Ayiriri: Jaruma Aisha Aliyu Tsamiya za ta shiga daga ciki a ranar Juma'a mai zuwa

  • Labarin da ke bayyana a yanzu shi ne batun amarcewar da jaruma Aisha Aliyu Tsamiya za ta yi a ranar Juma'a mai zuwa
  • An gano cewa za a daura auren jarumar a Masallacin Sheikh Salban da ke kwanan 'yan wanki kusa da gidan Tanko yakasai
  • Jaruman masana'antar masu tarin yawa kamar su Ali Nuhu, Zahrau Shata da sauransu sun dinga wallafa hotunanta tare da yi mata fatan alheri

Kano - Labari mai dadi da ke bayyana a masana'antar Kannywood shi ne batun auren fitacciyar jaruma Aisha Aliyu Tsamiya. Majiyoyi masu yawa sun tabbatar da cewa za a daura auren a ranar Juma'a mai zuwa.

Shafin Labaran Kannywood na Twitter ya fara wallafa labarin amma sai dai sun sanar da cewa jita-jita ce babu tabbaci. A wallafar da shafin yayi, ya ce:

Kara karanta wannan

Bayan watanni 11, Iyalan yan kasuwa canjin Kano da DSS ta kama sun ga mazajensu

"Mun samu jita-jitar cewa a ranar Juma'ar nan mai zuwa jaruma Aisha Tsamiya za ta amarce... Kuma angon nata babban mutum ne."
Jaruma Aisha Aliyu Tsamiya za ta shiga dàga ciki a ranar Juma'a mai zuwa
Jaruma Aisha Aliyu Tsamiya za ta shiga dàga ciki a ranar Juma'a mai zuwa. Hotuna daga @realalinuhu @zahraushata
Asali: Instagram

Duk da bahaushe na cewa, in ka ji gangami, toh tabbas akwai labari. Hakan yasa Legit.ng ta garzaya domin nemo muku bayani mai gamsarwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A matakin farko, Legit.ng ta fada kafar sada zumuntar zamani ta Instagram inda ta fara bin shafukan abokan sana'arta.

A karon farko, mun ci karo da wallafar jarumi Ali Nuhu inda ya saka hoton jarumar tare da yi mata fatan alheri.

Ya ce: "Allah yasa alheri daughter"

Baya ga nan, Legit.ng ta ci karo da wallafar tsohuwar jarumar masana'antar, Zahrau Shata, inda ta saka hoton Aisha Tsamiya sannan ta rubuta:

"Allah ya sanya alkhairi kanwata."

A wallafar da shafin KanyywoodCelebrities ta yi, ta saka katin daurin auren sannan ta yi rubutun sanarwar amma daga bisani an cire shi. Ga abinda ya kunsa:

Kara karanta wannan

Adashin N2,000 take kullum: Jami'ai kan mabaraciyar da aka kama da N500,000 da $100 a Abuja

"Za a yi bikin Aisha Aliyu Tsamiya, ranar Juma'a 25 ga watan Fabrairu a masallacin Sheikh Salban, kwanan 'yan wanki kusa da gidan Tanko Yakasai. Muna rokon Allah yasa albarka kuma ya basu zaman lafiya. Amin ya Allah.

Bidiyo da hotunan Jaruma Laila ta cikin shirin Labarina yayin da ta yi aure

A wani labari na daban, labari da ke bayyana da dumi-duminsa a safiyar Asabar din nan shi ne na auren jarumar shiri mai dogon zango na Labarina. Mai bayar da umarni na shirin Labarina, Malam Aminu Saira ne ya wallafa bidiyo tare da taya jarumar murnar auren da ta yi a madadin kansa da kamfanin Saira Movies.

Kamar yadda wallafar da @aminusaira yayi ta bayyana:

"A madadi na da kamfanin sairamoviestv, muna taya 'yar uwa Maryam Waziri murnar auren da ta yi a yau, wato Juma'a. Allah ya ba su zaman lafiya, Allah ya ba su zuriya dayyiba. Muna taya ki murna, muna kewar ki Laila"

Kara karanta wannan

Kotun shari'a ta sa an jefe mace da namiji bayan an kama su dumu-dumu suna lalata

Asali: Legit.ng

Online view pixel