Bidiyo da hotunan Jaruma Laila ta cikin shirin Labarina yayin da ta yi aure

Bidiyo da hotunan Jaruma Laila ta cikin shirin Labarina yayin da ta yi aure

  • Jaruma Maryam Waziri a shiri mai dogon zango na Labarina, wacce aka fi sani da Laila Labarina ta yi aure a ranar Juma'a
  • Kamar yadda Malam Aminu Saira, daraktan shirin ya wallafa a shafinsa na Instagram, ya taya ta murna tare da mata addu'o'i
  • Har a halin yanzu dai ba a san waye mai sa'an da yayi wuf da zukekiyar jarumar ba don kuwa babu hotunan bikin a bayyane

Labari da ke bayyana da dumi-duminsa a safiyar Asabar din nan shi ne na auren jarumar shiri mai dogon zango na Labarina.

Mai bayar da umarni na shirin Labarina, Malam Aminu Saira ne ya wallafa bidiyo tare da taya jarumar murnar auren da ta yi a madadin kansa da kamfanin Saira Movies.

Kara karanta wannan

Magidanci ya nemi kotu ta raba auren shekaru 19 saboda matarsa na 'sheƙe aya' da mai maganin gargajiya

Bidiyon Jaruma Laila ta cikin shirin Labarina yayin da ta yi aure
Bidiyon Jaruma Laila ta cikin shirin Labarina yayin da ta yi aure. Hoto daga @aminusaira
Asali: UGC

Kamar yadda wallafar da @aminusaira yayi ta bayyana:

"A madadi na da kamfanin sairamoviestv, muna taya 'yar uwa Maryam Waziri murnar auren da ta yi a yau, wato Juma'a. Allah ya ba su zaman lafiya, Allah ya ba su zuriya dayyiba. Muna taya ki murna, muna kewar ki Laila"

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bidiyon Jaruma Laila ta cikin shirin Labarina yayin da ta yi aure
Bidiyon Jaruma Laila ta cikin shirin Labarina yayin da ta yi aure. Hoto daga @aminusaira
Asali: Instagram

Ga mabiya shirin fim mai dogon zango na Labarina da kamfanin Saira Movies ke yi, sun san cewa jaruma Maryam Waziri wacce aka sani da Laila a shirin ta dade ba ta fitowa.

Babu shakka an yi makonni ba a ganin ta tun bayan da aka nuna ta tafi kasar waje karatu a shirin. Sai kwatsam labarin auren ta ya bayyana.

Ba wannan bane karo na farko da jarumar fim ke auren kwatsam kuma a sirrance ba. Ko a makonni kadan da suka gabata, Hajiya Rabi Bawa Mai Kada ta cikin shiri mai dogon zango na Kwana Casa'in ta shiga daga ciki.

Kara karanta wannan

Innalillahi: An tsinta gawar limamin Abuja kusa da gona

Duk da jarumar ta bayyana cewa, za a cigaba da ganin ta a cikin shirin Kwana Casa'in din.

Jaruma Rahama MK, matar gwamna a fim din Kwana Casa'in ta yi auren sirri

A wani labari na daban, ana tsaka da more shiri mai dogon zango na Kwana Casa’in sai aka wayi gari da batun auren sirri da wata jarumar fim din ta yi.

Jaridar Dimokardiyya ta ruwaito cewa, Rahama MK, wacce ta fito a matsayin matar Gwamna Bawa Mai Kada ta yi auren ta a ranar Asabar 6 ga watan Nuwamba.

Rahotanni sun nuna yadda aka yi shagalin bikin a gidan su da ke cikin garin Kano cike da sirri don ba kowa ya sani ba. Tuntuni an samu labari a kan batun auren jarumar amma ba ta fadi lokaci da kuma wanda za ta aura ba, hakan ya sa mutane su ka dinga mamaki.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel